2027: NNPP Ta Amince Da Bukatar Atiku Na Yin Hadaka, Ta Gindaya Sharuda Masu Tsauri

2027: NNPP Ta Amince Da Bukatar Atiku Na Yin Hadaka, Ta Gindaya Sharuda Masu Tsauri

  • A karshe, jam'iyyar NNPP ta amince da bukatar dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar
  • Jam'iyyar ta ce ta gamsu da kiran tsohon shugaban kasar amma ta gindaya sharudan don ganin an samu daidaito a tsakani
  • Legit Hausa ta ji ta bakin Sakataren jam'iyyar NNPP reshen jihar Gombe kan wannan mataki na jam'iyyar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Jami'yyar NNPP ya amince da tayin dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar na hadaka.

Wannan na zuwa ne bayan Atiku ya nemi 'yan jam'iyyun adawa da su zo a hada kai don kwato mulki daga APC mai mulki.

Jam'iyyar NNPP ta amince da hadaka da Atiku ya kira don tumbuke APC
Jam'iyyar NNPP ta amince da bukatar Atiku kan maja. Hoto: Atiku Abubakar, Peter Obi, Kwankwaso R.
Asali: Facebook

Mene bukatar Atiku ga jam'iyyun adawa?

Kara karanta wannan

Tsohon mataimakin gwamna da wasu jiga-jigan PDP 2 sun watsar da lema, sun mara wa gwamnan APC baya

Daga bisani, jami'yyar LP ta yi fatali da bukatar ta Atiku inda ta ce babu wata magana da su ka kulla ta maja, Tribune ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mukaddashin shugaban jam'iyyar, Abba Kawu Ali shi ya bayyana haka ga manema labarai a yau Talata 21 ga watan Nuwamba.

Kawu ya ce NNPP ta shirya yin 'maja' da dukkan jam'iyyun adawa amma da sharadin duba bukatun al'umma da dimukradiyya.

Ya ce kiran da Atiku ya yi abun a yaba ne ganin yadda jami'yyar APC ke son mayar da kasar tsarin jam'iyya daya, Vanguard ta tattaro.

Mene martanin NNPP kan bukatar Atiku?

Ya ce:

"Kwanan nan Atiku ya kirayi maja tsakanin jam'iyyun adawa don ruguza tsarin jami'yya daya da APC ke yi a kasar.
"Jam'iyyar NNPP ta karbi wannan kira na Atiku a matsayin kishin kasa kuma abin a yaba.

Kara karanta wannan

Kano: Yayin da CTC ta tabbatar da nasarar Abba Kabir, NNPP ta fadi hanyar warware matsalar

"Mu na maraba da wannan kira na tsohon shugaban kasa, sai dai dole tsarin ya zamo zai amfani ga bukatun al'umma."

Legit Hausa ta ji ta bakin Sakataren jam'iyyar NNPP reshen jihar Gombe, Nasir Muhammad Baba Sherrif.

Sherrif ya ce maganan kiran Atiku Abubakar na hadin kai wannan abin yabawa ne inda ya ce su na goyon bayan hakan dari bisa dari.

Ya ce:

"Jam'iyyarmu ta fitar da sanarwa akan cewa a zo a yi 'maja' bisa wasu sharuda, tabbas mu a matakin jihar ba abin da za mu fada sabanin abin da uwar jam'iyya ta ce.
"Mu na tare da wannan mataki kuma wannan hadaka za ta da gagarumar nasara a zaben da ke tafe wanda zai kawo karshen APC da gyara kuskuren da aka yi a baya."

Atiku ya bukaci yin maja don tunbuke APC

A wani labarin, dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya bukaci hadin kan jam'iyyun adawa don kwace mulki a hannun APC.

Wannan na zuwa ne bayan Shugaba Tinubu ya yi nasara a kotun koli kan shari'ar da jam'iyyun adawa su ka shigar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel