Ramuwar Gayya: APC Ta Gamu da Babbar Mastsala Yayin da Jam’iyyun Siyasa 7 Suka Hade Kansu

Ramuwar Gayya: APC Ta Gamu da Babbar Mastsala Yayin da Jam’iyyun Siyasa 7 Suka Hade Kansu

  • Jam'iyyun adawa bakwai ne suka hada kansu karkashin kungiyar hadakar jam'iyyu (CCPP) don kawo karshen mulkin APC a Najeriya
  • Jam'iyyun sun hada da PDP, NNPP, ADC, APM, SDP da kuma ZLP, wadanda suka yi yakinin hadakar za ta bunkasa dimokuradiyya
  • Sai dai jam'iyyar APC ba ta ce uffan kan hadakar ba, amma Farfesa Fage ya ce hadakar ba za ta je ko ina ba ma damar APC ta tashi tsaye

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Babbar jam'iyyar adawa ta PDP, NNPP da wasu jam'iyyun siyasa biyar sun hade kansu don yin aiki karkashin inuwa daya.

Jam'iyyun da suka shiga hadakar sun hada da ADC, APM, SDP da kuma ZLP, inda aka sanya wa tafiyar suna ‘the Coalition of Concerned Political Parties (CCPP)’, watakan hadakar jam'iyyun siyasa da suka damu da halin da Najeriya ke ciki.

Kara karanta wannan

Jigon NNPP ya fadi dalili 1 da ya sa masu ruwa da tsakin jam'iyyar suka tabbatar da korar Kwankwaso

Peter Obi/Atiku Abubakar/Abba Kabir Yusuf
Jam'iyyar PDP, NNPP, ADC, APM, SDP da kuma ZLP sun hade kai, wadanda suka yi yakinin hadakar za ta bunkasa dimokuradiyya. Hoto: Peter Obi, Atiku Abubakar, Abba Kabir Yusuf
Asali: Twitter

A watan da ya gabata ne Legit Hausa ta ruwaito maku tayin da Atiku Abubakar ya yi wa jam'iyyun siyasa na hada kai don murkushe jam'iyya mai mulki ta APC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tun a lokacin shugabannin jam'iyyu biyu: LP da NNPP suka bayyana cewa hadakar na da matukar muhimmanci don kawo karshen gwamnati mai ci a yanzu, rahoton Daily Trust.

Ba maja ba ce, CCPP ta yi karin haske

Da ya ke jawabi ga manema labrai bayan taron jam'iyyun bakwai, shugaban SDP, Shehu Gabam, ya ce ba maja ba ce, kawai hadaka ce don neman mafita kan abokin adawa daya.

Leadership ta ruwaito sakataren riko na PDP, Setonji Koshoedo, ya bayyana cewa hadakar za ta ba jam'iyyun adawa karfin da za su kawo karshen matsalolin Najeriya.

Shugaban jam'iyyar ADC na kasa Chief Ralph Nwosu, ya ce hadakar za ta karfafa dimokuradiyya, yayin da shi ma shugaban APM, Yusuf Dantalle ya ce akwai jam'iyyun da ke cikin hadakar da ba su samu halartar zaman ba.

Kara karanta wannan

Kus-kus: Ganduje ya shiga ganawar sirri da Gwamna Mai Mala Buni, Ubah da wasu jiga-jigan APC

Idan aka cire Gabam, Koshoedo, Nwosu da Dantalle, sauran wakilan jam'iyyu da suka halarci zaman sun hada da shugaban NNPP, Abba Kawu Ali; sakataren YPP, Egbbeola Martins da sakataren ZLP.

Bukatun jam'iyyun kan wannan hadaka

Gabam ya ce kungiyar hadakar ta na so fannin shari'a ya rinka yanke hukunci kan gaskiya, inda ya kawo misali da hukuncin Kotun Daukaka Kara a zaben jihohin Zamfara, Nasarawa, Kano da Filato, inda 'yan takarar jam'iyyun hadakar suka sha kasa.

Kungiyar hadakar ta kuma nuna damuwa kan yadda tsaro ke kara tabarbarewa a kasar, tare da neman majalisar dokokin tarayya ta sake duba kasafin 2024 da shugaba Tinubu ya gabatar.

APC ta yi kuma da bakin ta

A bangaren jam'iyya mai mulki kuwa, babu wani tsokaci kan wannan hadaka. Sakataren watsa labaran APC na kasa Felix Morka, bai amsa wayarsa ko mayar da sakonnin da aka aika masa ba.

Taron tsintsiya ne ba shara - Fage ya kalubalanci hadakar jam'iyyun

Kara karanta wannan

Gwamna ya matsawa EFCC ta kama tsohon ministan Buhari kan wasu dalilai, bayanai sun fito

Da ya ke tsokaci kan wannan hadaka, masanin siyasa, Farfesa Kamilu Sani Fage ya ce ikirarin jam'iyyun na cewa ba maja ba ce, kawai hadaka ce alama ce ta nuna taron ba zai je ko ina ba.

Fage ya ce hadakar ba za ta rasa nasaba da zaben 2027 mai zuwa nan da shekaru uku da rabi ba, inda yake hasashen hadakar na iya tarwatsewa kafin zaben, ma damar APC ta yunkura tun yanzu.

Sanata Shehu Sani: Sojoji sun koma kashe fararen hula?

A wani labarin, Sanata Shehu Sani ya ce harin bam da sojoji suka kai garin Tudun Biri a jihar Kaduna ba kuskure ba ne, ganganci ne da bai kamata ya faru ba.

A cewar sanatan, sojoji sun koma kaddamar da hare-hare kan fararen hula amma sun kasa dakile 'yan ta'addan da suka addabi kasar, Legit Hausa ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel