Gwamnan APC Mara Lafiya Ya Kashe N7.3bn a Lokacin Jinya? APC Ta Bayyana Gaskiya

Gwamnan APC Mara Lafiya Ya Kashe N7.3bn a Lokacin Jinya? APC Ta Bayyana Gaskiya

  • Jam’iyyar APC a jihar Ondo ta yi magana kan N7.3bn da ake zargin gwamna Rotimi Akeredolu ya kashe a lokacin da yake hutun jinya a ƙasar Jamus
  • SaharaReporters ta yi wannan zargin ne a wani rahoto da ta fitar, inda ta ƙara da cewa gwamnan ya amince da kuɗin ne a zaman da ya yi na watanni uku a Turai ba tare da amincewar majalisar dokokin jihar ba
  • Sai dai jam'iyyar ta bayyana cewa, kuɗaɗen da aka ware sun haɗa da na tallafin da aka samu daga gwamnatin tarayya kuma an kashe su ne ga al'ummar jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Akure, Ondo - Jam’iyyar APC reshen jihar Ondo ta mayar da martani kan zargin da ake yi na Gwamna Rotimi Akeredolu da ke fama da rashin lafiya ya kashe N7.3bn a tsakanin watannin Yuli da Satumba 2023 ba tare da amincewar majalisar dokokin jihar ba.

Kara karanta wannan

Matawalle vs Lawal: Gwamnan PDP ya faɗi wanda zai samu nasara a zaben da za a ƙarisa a Zamfara

Jaridar SaharaReporters, ta yi wannan zargin a cikin rahotonta, inda ta bayyana cewa Akeredolu ya amince da kuɗin ne a lokacin da yake hutun jinya a Jamus na tsawon watanni uku.

APC ta musanta batun cewa Akeredolu ya kashe N7.3bn
APC ta yi martani kan batun cewa Gwamna Akeredolu ya kashe N7.3bn ba tare da amincewar majalisa ba Hoto: Rotimi Akeredolu
Asali: Twitter

Yadda Gwamna Akeredolu ya kashe sama da N7bn yayin da yake hutun jinya

Tun da farko Gwamna Akeredolu ya bar ƙasar nan ne a ranar 7 ga watan Yuli domin hutun jinya na kwanaki 21 amma ya dawo ƙasar a watan Satumba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tun bayan dawowar sa, har yanzu bai cigaba da aikinsa ba, kuma rahotanni sun ce yana zaune a Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

Biyo bayan rahoton na SaharaReporters, jam’iyyar APC a jihar Ondo ta yi amfani da shafinta na Twitter a ranar Talata, 21 ga watan Nuwamba, inda ta yi ƙarin haske kan kuɗaɗen da aka kashe ba tare da amincewar majalisar dokokin jihar ba.

Kara karanta wannan

Akwai matsala: Babban malamin addini ya yi magana kan yiwuwar tsige Gwamna Ahmadu Fintiri na Adamawa

APC ta bayyana yadda Akeredolu ya kashe sama da N7bn cikin watanni uku

Jam’iyyar APC a jihar ta bayyana cewa ta dauki matakin ne domin yin ƙarin haske, inda ta ƙara da cewa adadin na kuɗin na tallafin da jihar ta samu daga gwamnatin tarayya ne.

Ta bayyana cewa, an ware kuɗaɗen ne a ƙarƙashin wani abu da ka iya zuwa wanda ba a yi tsammani ba, wanda ba a sanya shi a cikin kasafin kuɗin shekara ba.

Sanarwar ta ƙara da cewa:

"Gwamna Akeredolu bai kashe N7.3bn domin ƙashin kan sa ba, a maimakon haka, an yi amfani da waɗannan kuɗaɗen yadda ya kamata domin bayar da tallafi."
"Gwamnatin tarayya ce ta fitar da kuɗaɗen ga jihar a wani ɓangare na ƙoƙarin rage raɗaɗin cire tallafin man fetur a faɗin ƙasar nan."

An Ba Akeredolu Wa'adin Sa'o'i 72

A wani labarin kuma, Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo ya samu wa'adin sa'o'i 72 daga gamayyar ƙungiyoyin jam'iyyun adawa.

Gamayyar ƙungiyoyin a ƙarƙashin PDP Forever Initiative sun ba gwamnan wa'adin ne domin ya miƙa mulko ga mataimakinsa ko su mamaye gidan gwamnatin jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel