Daraktan Kamfen PDP Ya Yi Murna Bayan Shan Kaye da PDP Ta Yi a Kotu? Gaskiya Ta Fito

Daraktan Kamfen PDP Ya Yi Murna Bayan Shan Kaye da PDP Ta Yi a Kotu? Gaskiya Ta Fito

  • Labaran Maku, daraktan kamfen PDP a jihar Nasarawa ya karyata jita-jitar cewa sun yi farin ciki da hukuncin kotu a jiya
  • Ana zargin Maku da daraktan yada labarai na PDP, Mike Omeri da cewa sun raka Gwamna Sule ziyarar godiya ga shugaban APC, Ganduje
  • A cikin wata sanarwa, wadanda ake zargin sun barranta kansu da wannan lamari inda su ka bukaci mutane su yi watsi da labarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Darakta Janar na kwamitin kamfen PDP a jihar Nassarawa, Labaran Maku ya yi martani kan zargin murna a kotun koli.

Maku ya bayyana haka yayin da ake zarginshi da daraktan yada labarai na PDP, Mike Omeri cewa sun yi farin ciki da hukuncin kotun, cewar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Bayan shari'ar Nasarawa, kotu ta sake yanke hukunci kan shari'ar zaben gwamnan APC, ta ba da dalili

Maku ya yi martani kan zargin cewa sun yi farin ciki da hukuncin kotu a jihar Nasarawa
Labaran Maku ya yi martani kan zargin yin farin ciki a hukuncin kotu. Hoto: Labaran Maku.
Asali: Twitter

Wane hukunci kotun ta yanke?

A jiya ne kotun daukaka kara ta rusa hukuncin karamar kotu inda ta ayyana Gwamna Sule Abdullahi na APC a matsayin wanda ya lashe zabe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dan takarar jam'iyyar PDP, David Ombugadu na kalubalantar nasarar Sule a matsayin wanda ya yi nasara a zaben.

Rahotanni sun ruwaito cewa ana zargin Maku da Omeri sun raka Gwamna Sule zuwa wurin shugaban APC, Abdulllahi Ganduje don ta ya shi murna.

Wane martani su ka yi kan zargin?

A martaninshi, Omeri ya fitar da sanarwa inda ya bayyana labarin da kirkirarre don bata mu su suna.

Ya ce:

"Ina son yin amfani da wannan dama wurin tabbatar da cewa da ni da Labaran Maku babu wanda ya aikata abin da ake zargi kuma ba ma tare da abin da ake zargin mu da shi.

Kara karanta wannan

Yanzu yanzu: Kotun daukaka kara ta yanke hukunci kan zaben Gwamna Sule na Nasarawa

"Mu na mai tabbatar da cewa mun tsaya tsayin daka don ganin mun kwato hakkinmu da aka kwace na nasarar David Ombugadu."

Omeri ya bukaci al'umma da su yi watsi da wannan jita-jitar inda ya ce hakan na lalata karsashin dimukradiyya, Vanguard ta tattaro.

Shugaban jam'iyyar PDP a jihar, Mista Francis Orogu ya tabbatar da cewa za su daukaka kara don ganin an sauya wannan hukunci da aka yi kuskure.

Kotun ta bai wa Gwamna Sule nasara

Kun ji cewa, Kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja ta yi hukunci kan shari'ar zaben gwamnan jihar Nasarawa.

Kotun ta rusa hukuncin karamar kotun da ta bai David Ombugadu na jam'iyyar PDP nasara a watan Oktoba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel