Sabuwar ɓaraka ta kunno kai a APC, mambobin NWC 2 sun buƙaci a yi wa Sanata Adamu ta-waye

Sabuwar ɓaraka ta kunno kai a APC, mambobin NWC 2 sun buƙaci a yi wa Sanata Adamu ta-waye

  • Sabuwar baraka ta kunno kai a tsakanin shugabannin jam'iyyar APC ta kasa inda ake zargin Sanata Adamu da mulki shi kadai
  • Kamar yadda takardar da mataimakan shugaban jam'iyyar 2 suka fitar, sun bukaci NWC ta hade kai tare da ceto jam'iyyar
  • A cewar Lukman da Isaac, Adamu na yanke hukunci kuma ya alakanta shi da Buhari ta yadda babu mai iya kalubalantarsa

FCT, Abuja - Sabon rikici ya kunno kai a jam'iyyar APC yayin da mambobi biyu na kwamitin ayyuka na kasa, NWC, suka bukaci abokan aikinsu da su tashi tsaye tare da hade wa shugaban jam'iyyar na kasa, Sanata Abdullahi Adamu kai.

A wata takarda da ta fita a ranar Talata a Abuja, mataimakin shugaban jam'iyyar na kasa na yankin arewa maso yamma, Salihu Mohammed Lukman, da mataimakin jam'iyyar na kasa daga kudu maso yamma, Isaac Kekemeke, sun ja kunnen Adamu kan daukar mataki shi kadai da sunan shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan

2023: Buhari ya lissafa sharuddan da dole 'dan takarar shugabancin kasa na APC ya cika

Sabuwar ɓaraka ta kunno kai a APC, mambobin NWC 2 sun buƙaci a yi wa Sanata Adamu ta-waye
Sabuwar ɓaraka ta kunno kai a APC, mambobin NWC 2 sun buƙaci a yi wa Sanata Adamu ta-waye. Hoto daga @OfficialAPCNG
Asali: Twitter

Daily Trust ta rahoto cewa, an dage wani taron NWC sau biyu ba tare da wani dalili ba a lokacin da lamurran siyasa suka kai kololuwa.

Wani sashi na takardar ya bayyana cewa, "A matsayinmu na mambobin NWC da ke da alhakin mambobinmu, muna mika sanarwa ga Abdullahi Adamu, ta kuma hannun shi da ya kira dukkan mambobin APC kan cewa duk wani hukuncin da shugaban jam'iyyar zai yanke ko wani jigo, wanda ke bukatar amincewa kamar yadda kundin tsarin mulkin APC ya bukata, za a dauke shi ba bisa ka'ida ba kuma karantsaye ga dokar NWC, matukar NWC ko wasu daga cikin mambobin kwamitin shugabancin jam'iyyar ba su yarda da shi ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Babu mamban NWC da aka zaba a ranar 26 ga watan Maris don ya dumama ofishinsa a sakateriyar jam'iyya ta kasa. A don haka muna kira ga dukkan abokan aikinmu da su tashi tsaye kan wannan kalubalen ta hanyar hada karfi da karfe wurin ceto jam'iyyar mu da dawo da ita zuwa kan turbar da aka gina ta na kawo cigaban Najeriya cike da gaskiya, adalci da kuma jajircewa. Allah ya yi wa jam'iyyar mu albarka!

Kara karanta wannan

Shirin zaben fidda gwani: Tinubu, wasu 11 sun tsallake tantancewar shugabannin APC

"A cikin watanni biyu kacal na shugabancin da muka yi na jam'iyyar mu karkashin Sanata Abdullahi Adamu, NWC tana da karfin ikon kula da lamurran yau da kullum, har da yanke shawara na NEC kamar yadda sashi na 13, sakin layi na 4 na kundin tsarin mulkin APC ya bayyana.
"Shugaban jam'iyyar na daukar mataki shi kadai. A lokacin da ya ga dama, yana saka sunan shugaban mu, Shugaban kasa Muhammadu Buhari domin tirsasa mambobin NWC don su yarda da hukuncinsa. Duk wani kokari na ganin cewa shugaban ya mutunta shugabancin NWC kamar yadda aka zabe su a ranar 26 ga watan Maris, ya gagara. A kula cewa, karfin ikon NEC ga NWC ne kuma ba ga shugaban jam'iyyar ko wani ba.
"A matsayin mu na jam'iyya, mun fuskanci tozarci na shari'a da ke tasowa daga take dokar kundin tsarin jam'iyya. Ya zame mana dole mu fitar da wannan sanarwar ne saboda jerin yadda ake ta dage taron NWC, har sau biyu cikin sa'o'i 48."

Kara karanta wannan

Babbar magana: An bukaci kwamiti ya kori Tinubu daga takaran shugaban kasa a APC

Asali: Legit.ng

Online view pixel