Tinubu: Gaskiyar Dalilin Ganin ‘Mace’ a Takardar Karatun Shugaban Kasa Inji Lauya

Tinubu: Gaskiyar Dalilin Ganin ‘Mace’ a Takardar Karatun Shugaban Kasa Inji Lauya

  • Ta tabbata cewa akwai alamar mace a wasu daga cikin takardun shaidar Bola Ahmed Tinubu
  • Lauyan Mai girma shugaban kasan ya shaida cewa tangarda kurum aka samu daga jami’ar CSU
  • Wole Afolabi ya wanke Tinubu tsaf daga duk wasu zargin da masu tuhuma su ke yi wa shugaban

Abuja - Bola Ahmed Tinubu ya na cigaba da yin karin haske a game da sabanin da aka samu dangane da takardun shaidar karatunsa.

A wata hira da aka yi da lauyan shugaban kasar wannan karo, Wole Afolabi ya yi wa tashar Channels TV bayanin abin da ya je ya dawo.

Wole Afolabi ya ce tangardar da aka samu daga jami’ar jihar Chicago da ke Amurka ne dalilin ganin satifiket ya na dauke da alamar mace.

Kara karanta wannan

Atiku Ya Fadi Yadda Buhari Ya Durkusar da Kasuwancinsa Wajen Fallasa Tinubu

Shugaban kasa
Shugaban kasa Bola Tinubu Hoto: Asiwaju Bola Tinubu
Asali: Facebook

Lauya ya ce Bola Tinubu bai da laifi

Daily Trust ta rahoto Afolabi ya na mai kare shugaba Tinubu a kan batun ‘Afolabi’ da ake zargin ya fito a takardunsa na karatun sakandare.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Afolabi ya ce jami’ar ta CSU ta tabbatar da cewa Bola Tinubu ne dai dalibin da aka ba gurbin karatu bayan ya halarci Southwest College.

"A zahiri yake, duk wasu bayanai sun nuna. An yi wa magatakardar jami’ar tambaya a game da dalilin sabani kan bayanan Bola Tinubu.
Magatakardan ya ce mai neman gurbin karatun ya tabbatar da cewa shi namiji ne ba mace ba a lokacin da aka ba shi takardar shiga jami’a.
Da aka jefawa Dr West Brown tambaya, ya ce ba abin mamaki ba ne jami’o’i su samu kuskuren alkalami.

- Wole Afolabi

Daily Post ta ce lauyan ya kara nuna da kamar wahala wanda ya ba shugaba Tinubu takardar shaida a 1979 a ce ya na aiki a jami’ar har zuwa yau.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Atiku Ya Bayyana Abu 1 Rak Da Zai Sa Ya Haƙura Ya Daina Yaƙar Shugaba Tinubu

Game da bambanci game da hannu, lauyan ya ce makaranta ba ta sa hannu a lokacin da aka kammala karatu sai lokacin da aka nemi takarda.

Ba na tsoron kowa Inji Atiku

Wazirin Adamawa ya bude shafin da bai saba budewa ba, ya yi maganar hanyar neman kudinsa da gwamnatin Muhammadu Buhari ta toshe.

Da yake jawabi, an rahoto Atiku Abubakar ya ce Gwamnatin Buhari ta karbe kwangilarsa da kamfanonin mai kuma ta rabawa mutanenta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel