Gwamna Sanwo-Olu Ya Sauya Wa Wasu Hadimansa Wurin Aiki a Jihar Legas

Gwamna Sanwo-Olu Ya Sauya Wa Wasu Hadimansa Wurin Aiki a Jihar Legas

  • Mista Babajide Sanwo-Olu ya canza wa wasu daga cikin masu ba shi shawara ta musamman ma'aikatun da za su yi aiki
  • Gwamnan Sanwo-Olu na Legas ya sanar da sauye-sauyen ne a wurin taron maraba da aka shirya wa sabbin mambobim majalisar zartarwa
  • A ranar Laraba da ta gabata gwamnan ya rantsar da kwamishinoni da hadimai bayan dogon lokacin ana taƙaddama da majalisar dokoki

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Lagos - Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya sauya wa wasu daga cikin mambobin majalisar zartarwansa ma'aikatar da zasu yi aiki, Guardian ta rahoto.

Gwamnan ya sanar da sunayen waɗanda ya canza wa mukamin ne a ranar Juma’a a wurin taron aka saba shirya musu tare da manyan sakatarori na 2023.

Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo Olu.
Gwamna Sanwo-Olu Ya Sauya Wa Wasu Hadimansa Wurin Aiki a Jihar Legas Hoto: Governor Babajide Sanwo-Olu
Asali: Twitter

Mista Sanwo-Olu ya canza Dokta Oreoluwa Finnih daga matsayin mashawarci na musann kan ma'aikatar lafiya ya maida shi muƙamin mai bada shawara kan manufofin ci gaba (SGDs).

Kara karanta wannan

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un, Mummunan Ibtila'i Ya Laƙume Rayukan Mata 5 a Cikin Mota

Haka nan ya ɗauke Abiola Olowu daga mai bada shawara ta musamman na ma'aikatar kasuwanci, ciniki da zuba hannun jari, ya maida shi mashawarci na musamman a ma'aikatar makamashi da ma'adanai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda gwamnan ya naɗa muƙarrabansa

Jaridar PUNCH ta rahoto cewa gwamna Sanwo-Olu, a ranar Laraba, ya rantsar da kwamishinoni 37 da masu ba da shawara na musamman.

The Cable ta ce bikin rantsarwar wanda ya gudana a dakin taro na Adeyemi Bero dake Alausa, Ikeja, ya tabbatar da kaddamar da majalisar zartarwan gwamnan a karo na biyu.

Idan zaku iya tunawa yayin tantance sunayen gwamnanm Sanwo Olu ya naɗa, majalisar dokokin jihar Legas ta yi watsi da wasu daga cikin mutane da ya aiko mata.

Duk da ja in ja da aka yin naɗin kwamishinonin, daga ƙarshe majalisar ta amince da naɗa mutane 38 yayin na baya shi ne Tolani Akibu, wanda ya samu shiga awanni 24 gabanin bikin rantsarwa.

Kara karanta wannan

"Abinda Ya Sa Iyaye Suka Daina Tura 'Ya'yansu Makarantu a Najeriya" Ministan Tinubu Ya Magantu

Shugaba Tinubu Ya Naɗa Sabon Gwamnan Babban Banki CBN da Mataimaka 4

A wani rahoton na daban kun ji cewa Bola Ahmed Tinubu ya amince da naɗa Dakta Olayemi Michael Cardoso a matsayin sabon gwamnan babban banki CBN

Shugaban ƙasar ya kuma naɗa mataimakan gwamnan guda huɗu duka na tsawon shekaru 5 idan majalisar dattawa ta tabbatar da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262