Gwamnati Ta kafa Kwamitin Mutane 15 Ya Shirya Bikin Cika Shekara 63 da ‘Yanci

Gwamnati Ta kafa Kwamitin Mutane 15 Ya Shirya Bikin Cika Shekara 63 da ‘Yanci

  • An kafa kwamiti na musamman wanda zai yi aikin tsara bukukuwan murnar samun ‘yancin-kai
  • Kwamitin ya kunshi ministocin tarayya, jami’an gwamnati da manyan shugabannin tsaro na kasar nan
  • A ranar 1 ga Oktoba Najeriya za ta cika shekara 63 da samun ‘yancin kai a hannun turawan Birtaniya

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - A ranar 1 ga watan Oktoban 2023, Najeriya za ta cika shekaru 63 da samun ‘yancin kai daga hannun turawan mulkin mallaka.

A sanadiyyar haka, za a gudanar da bukukuwa na musamman kamar yadda aka saba, FRCN ta ce an kafa kwamiti da zai tsara bikin bana.

An rantsar da wani kwamitin musamman na ministoci da zai yi aikin shiryen bikin shekarar nan, wanda za a gudanar nan da makonni biyu.

Gwamnatin tarayya
Ministocin gwamnatin tarayya Hoto: @SGFAkume
Asali: Twitter

'Yan kwamitin bikin 'yancin-kai

Kara karanta wannan

Shari’ar zabe, 50% da Hanyoyi 3 da Za a Iya Bi Wajen Gyara Zabe – Ministan Jonathan

‘Yan kwamitin sun fito ne daga ma’aikatun yada labarai da wayar da kan al’umma, harkokin cikin gida, tattalin arziki sai harkokin ketare.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ragowar ‘yan kwamitin sun kunshi jami’an babban birnin tarayya na Abuja, mai ba shugaban kasa shawara a kan harkar tsaro da kuma IGP.

Bayan da aka samu daga tashar rediyon tarayyan ta ce a kwamitin akwai Shugaban hukumar DSS, da sojan da ke gadin fadar shugaban kasa.

Kwamitin ya kunshi manyan sakatarorin ma’aikatu irinsu kiwon lafiya, harkar tattalin arziki da siyasa da kuma ofishin harkoki na musamman.

George Akume ya rantsar da kwamiti

Da yake rantsar da kwamitin a ranar Alhamis, Daily Trust ta rahoto Dr. George Akume ya na cewa hakan zai bada damar tunawa da mazan jiya.

A sanadiyyar wannan biki da za a shirya a Abuja, sakataren gwamnatin tarayya ya ce za a tuna da wadanda su ka bautawa kasar a shekarun baya.

Kara karanta wannan

Jerin Ministocin Tinubu Da Kotun Zabe Ta Ayyana a Matsayin Wadanda Suka Lashe Zaben Yan Majalisun Tarayya

Akume wanda shi ne shugaban kwamitin, ya ce sai an zauna an yanke shawara kafin a amince da duk wani aiki da ‘yan kwamitin su ka kawo.

Za a gudanar da jawabi na musamman da laccoci kafin shugaban kasa ya yi bayani, sannan sai a rufe da fareti ranar 2 ga watan Oktoban nan.

Binciken tsohon babban banki

Rahoto ya nuna mutanen tsohon Gwamnan babban bankin CBN Godwin Emefiele za su iya samun kan su a matsala a sakamakon bincike da ake yi

Ba komai ya jawo hakan ba sai binciken da Jim Obazee yake yi wanda zai shafi ayyukan shekara da shekaru da aka yi a CBN da hukumar NIRSAL.

Asali: Legit.ng

Online view pixel