Tsaffin Yan Takarar Shugaban Kasa Sun Nemi Tinubu Ya Basu Mukami, Bayanai Sun Fito

Tsaffin Yan Takarar Shugaban Kasa Sun Nemi Tinubu Ya Basu Mukami, Bayanai Sun Fito

  • Yayin ganawa da shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi Ganduje, 'yan takarar shugaban kasa sun roki mukamai
  • 'Yan takarar sun roki Ganduje da ya bayyanawa Shugaba Tinubu bukatarsu ta neman mukami
  • Shugaba Tinubu tun farko ya roki 'yan adawa da su zo a yi gwamnatin hadaka don ciyar da kasa gaba

FCT, Abuja - Tsoffin 'yan takardar shugaban kasa a zaben da aka gudanar a watan Faburairu sun roki Shugaba Tinubu mukamai a gwamnatinsa.

Duba da yadda Shugaba Tinubu ya kira 'yan adawa da a zo ayi gwamnatin hadaka, hakan ya bai wa wasu 'yan jam'iyyu damar shiga gwamnatinsa, Legit.ng ta tattaro.

'Yan takarar shugaban kasa sun roki mukamai a wurin Tinubu
Yadda 'Yan Takardar Shugaban Kasa Su Ka Roki Tinubu Mukamai A Gwamnati. Bola Ahmed Tinubu.
Asali: Facebook

Meye 'yan takarar ke nema gun Tinubu?

'Yan takaran shugabn kasar sun bayyana haka yayin ganawa da shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi Umar Ganduje a yau Alhamis 31 ga watan Agusta.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Gana da Tsohon Gwamnan Jihar Arewa a Aso Villa, Sahihan Bayanai Sun Fito

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

'Yan takarar sun fito daga jam'iyyun APGA da ADP da NRM da APP da sauransu.

Sun bayyana cewa sun ki shiga shari'ar zaben shugaban kasa ne saboda kishin kasa tare da barin Shugaba Tinubu mai da hankali a kan ayyukan raya kasa.

Kakakin kungiyar 'yan takarar kuma dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar NRM, Ambasada Felix Johnson Osakwe ya tabbatarwa Bola Tinubu cewa su na tare da shi.

Sun ba da tabbacin goyon baya wa Tinubu

Sun kuma tabbatarwa jam'iyyar APC da shugabanninta goyon baya dari bisa dari don ciyar da Najeriya gaba, cewar Vanguard.

Idan ba a mantaba, sabon ministan Abuja, Nyesom Wike dan jam'iyyar adawa ne daga PDP wanda shugaban kasa, Bola Tinubu ya bai wa mukamin minista.

Jam'iyyar PDP ta yi barazanar dakatar da shi bisa zargin yi mata zagon kasa tare da hada kai da gwamnatin APC mai mulki.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Sake Ware Biliyoyin Kudade Don Sake Gina Arewa, Ya Bayyana Dalili

Tinubu Ya Ware Naira Biliyan 50 Don Sake Gina Arewacin Najeriya

A wani labarin, shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya ware makudan kudade har Naira biliyan 50 don sake gina Arewacin Najeriya da rashin tsaro ya musu katutu.

Mataimakin shugaban kasar, Kashim Shettima shi ya bayyana haka a yau Alhamis 31 ga watan Agusta a Abuja yayin wata ganawa.

Tinubu ya roki 'yan Najeriya da su yi hakuri da irin tsare-tsarensa inda ya ba su tabbacin cewa za su fi kowa morar hakan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel