Oscar 442 Sun Dace, Abba Ya Raba Mukamai Fiye da 60 a Awanni 12 a Kano

Oscar 442 Sun Dace, Abba Ya Raba Mukamai Fiye da 60 a Awanni 12 a Kano

  • Gwamnatin jihar Kano a karkashin jagorancin Abba Kabir Yusuf ta fitar da nadin wasu mukamai
  • Mai girma Gwamna ya bayyana cewa ya bada mukaman ne domin jawo matasa cikin gwamnati
  • Kamar yadda sanarwa su ka nuna sababbin mukamai da aka fitar a yammacin Litinin sun doshi 67

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Kano - Sanusi Bature Dawakin Tofa ya ce Abba Kabir Yusuf ya nada Manyan masu taimakawa (SSA) da masu taimakawa (SA) a gwamnati.

Ga jerin wadanda aka ba mukaman nan kamar haka:

1. Yusuf Ibrahim Sharada – SSA a bangaren fasahar zamani na ICT

2. Muhammad Sani Hotoro (Dan Sani) – SSA a kan harkar kungiyoyin ‘yan kasuwa

3. Barr. Nura Abdullahi Bagwai – SSA a kan harkar shari’a

4. Hon. Surajo Kanawa – SSA a harkar jawo kan al’umma (Kudancin Kano)

Kara karanta wannan

Malami: ICPC Sun Taso Lauyan Mai Auren ‘Yar Tsohon Shugaban kasa Buhari a Gaba

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

5. Muhd Sani Salisu Rimingado - SSA a harkar jawo kan al’umma (Arewacin Kano)

6. Nuhu Isa Gawuna - SSA a harkar jawo kan al’umma (Tsakiyar Kano)

7. Akibu Isa Murtala – SSA a Ofishin COS

8. Muhmud Tajo Gaya – SSA a wayar da kai na kiwon lafiya

9. Akibu Shehu Haske – SSA a kan gidajen jaridu

10. Bashir Sanata Sharada – SSA a kan yada labarai

Abba Gida Gida
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf Hoto: Sanusi Bature Dawakin-Tofa
Asali: Facebook

11. Jamilu Batayya – SSA a kan cigaban kasuwanci

12. Yahuza Adamu Yankaba – SSA a kan tashoshin mota

13. Kabiru Labour Kankarofi – SA a kan tashoshin mota

14. Lurwanu Kanwa – SAA a kan raya karkara

15. Aminu Iliyasu – SSA a kan tattalin arziki

16. Hassan Muhd Sadiq - SSA a kan kare masu sayan kaya

17. Engr. Shehu Shemo – SSA I a kan bibiyar ayyuka

18. Abdurraman Abubakar Gobirawa – SSA I a kan kasuwanni

Kara karanta wannan

Yanzu Nan: Abba Gida Gida Ya Yi Sababbin Nade-Naden Mukamai 15 a Jihar Kano

19. Barr. Sadiq Sabo Kurawa – SSA a kan harkokin shari’a

20. Engr. Abduljabbar Muhammad Nanono – SSA a kan lantarki da makamashi

Tijjani Gwandu da Oscar 442

21. Ibrahim Muhd Tukur Giginyu – SSA a kan fitilun hanya

22. Jamilu Lawan Saji - SSA a kan ayyuka na musamman I

23. Raji Hamisu Musa - SSA a kan ayyuka na musamman III

24. Aminu Imam Wali, Senior Special Assistant (SSA), KNARDA

25. Ibrahim Umar - SSA a kan tsaro

26. Tijjani Hussain Gandu - SSA a kan harkar da mawallafa

27. Sunusi Hafiz (Oscar 442) - SSA a kan harkar Kannywood

28. Sani Igwe - SSA a kan kasuwar waya

29. Garba Maisalati Garko - SSA a kan harkar sufuri

30. Alaramma Idris Ishaq Tarauni - SSA a kan harkar Islamiyyu

Bintoto, Jankunne da Adhama sun samu mukamai a Kano

31. Zakari Usman Balan – SSA a kan ban ruwa

32. Abdullahi Tank Galadanchi – SSA a kan harkokin rediyo

Kara karanta wannan

Maryam Shetty: ‘Yan Siyasa, ‘Yan Takara Da Mutane 5 Da Suka Ga Samu Da Rashi

33. Lt. Mohd Usaini Dadin Kowa – SSA a kan sha’anin sojoji

34. Fara'a Ibrahim Rogo - SSA a kan harkar kasuwancin mai

35. Maryam Abubakar Jankunne - SSA a kan tattaro matan karkara

36. Hafsat Aminu Adhama - SSA a kan ilmin ‘yan mata

37. Binta Zakari (Bintoto Kofar Ruwa) - SSA a kan wayar da kan mata

38. Abdullahi Ahmad Namama - SSA a kan sha’anin gwamnati da kasashen waje

39. Abbah Dala - SSA a kan wayar da kan al’umma

40. Babangida Sa'id (IBB) - SSA a kan Marshalls

41. Isa Musa Kumurya – SSA a kan Marshall na Jam’iyya

42. Yahaya Musa Kwankwaso - (DCoP) a ofishin Gwamna

Hadimai da shugabanni 25

Kafin nan Sanusi Dawakin Tofa ya bada sanarwar nada shugabannin hukumomi da jerin mutane 10 da za su zama masu bada shawara na musamman.

Bayan nan kuma a jiya ne aka sake nada mutane 15 a cikin jerin wadanda za su rika bada shawara.

Air Commodore Yusha'u Salisu Tudunwada Wada mai ritaya, Shema'u Aliyu, Dr. Sulaiman Wali Sani, Farfesa Auwalu Arzai su na cikin wadannan sahu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel