Tinubu Ya Janye Maryam Shetty, Ya Maye Gurbinta Da Mariya Maigari Mahmud Daga Kano

Tinubu Ya Janye Maryam Shetty, Ya Maye Gurbinta Da Mariya Maigari Mahmud Daga Kano

  • A karshe Shugaba Bola Tinubu ya zabi Festus Keyamo, tsohon karamin ministan kwadago a gwamnatin tsohon Shugaba Muhammadu Buhari
  • Shugaban kasar ya kuma janye zaben Maryam Shetty daga Jihar Kano kuma ya maye gurbinta da Dakta Mairiga Mahmud
  • Mahmud tsohuwar kwamishina ne na karatun makarantun gaba da sakandare a jihar Kano karkashin gwamnatin Gwamna Abdullahi Ganduje, shugaban jam'iyyar APC na kasa na yanzu

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari ya aika wani wasika ga majalisar dattawa, yana mai sanar da janye sunan Maryam Shetty tare da maye gurbinta da Mairiga Mahmud.

A sabon sakon, shugaban kasar ya kuma zabi Festus Keyamo, tsohon karamin minista a gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari don ya wakilci jihar Delta.

Tinubu ya cire Maryam Shetty ya maye gurbinta da Mariya Mahmud
Tinubu ya cire sunan Maryam Shetty daga cikin wadanda ya ke son nada wa minista. Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Abin da Shugaba Tinubu Ya Fada Mana a Aso Villa Inji Shugabannin ‘Yan Kwadago

Yadda Tinubu ya zabi ministan Buhari

Keyamo kuma ya yi aiki a matsayin mai magana da yawun kwamitin kamfen din zaben shugaban kasa na Bola Tinubu a zaben ranar 25 ga watan Fabrairu.

Godswill Akpabio, shugaban majalisar dattawan Najeriya ne ya sanar da hakan yayin zaman majalisar a ranar Juma'a 4 ga watan Agusta.

Abin da ya kamata ka sani game da Mairiga Mahmud, sabuwar wacce Tinubu ya zaba don nada ta minista daga Kano

Mairiga Mahmud, sabuwar wacce aka zaba minista daga Kano, ta yi aiki a matsayin kwamishiniya ta karatun makarantun gaba da sakandare karkashin tsohon gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje a wa'adinsa na biyu.

A ranar Alhamis, 3 ga watan Agusta ne aka zabi Ganduje a matsayin shugaban jam'iyyar APC na kasa yayin zabe karo na 12 na jam'iyyar.

Shugaba Tinubu, a ranar Alhamis, 27 ga watan Yuli, ya mika sunaye 28 da ya ke neman majalisa ta amince masa nada su minista.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Firai Ministan Canada Justin Trudeau Ya Saki Matarsa Bayan Shekaru 18

Bayan zaben Keyamo, jimillar wadanda aka zaba don nada su minista ya kai 48.

Gidan Talabijin na kasa, NTA, a ranar Juma'a 4 ga watan Agusta ya wallafa hakan. Ga sakon a kasa:

Yadda Maryam Shetty Ta Samu Labarin Cire Sunanta Tana Cikin Zauren Majalisa

Tunda farko, kun ji cewa Maryam Shetty tana cikin zauren majalisar dattawa a lokacin da ta samu labarin cire sunanta daga jerin ministoci.

Maryam Shettima, wacce aka fi sani da suna Maryam Shetty, tana ɗaya daga cikin sunayen ministoci 19 da shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya miƙa majalisa ranar Laraba, 2 ga watan Agusta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel