Oshiomole Ya Ce N30,000 Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi Ta Yi Kadan, Yana Biyan Mai Yi Masa Shara N60,000

Oshiomole Ya Ce N30,000 Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi Ta Yi Kadan, Yana Biyan Mai Yi Masa Shara N60,000

  • Sanatan Edo ta Arewa, Adams Oshiomole ya ce naira 30,000 a matsayin mafi ƙarancin alabashi ta yi kaɗan a Najeriya
  • Ya ce mai yi masa shara a gida ma naira 60,000 yake ba ta a matsayin albashi duk watan duniya
  • Oshiomole ya kuma bayyana cewa ma'aikatan kamfanoni masu zaman kansu sun fi ma'aikatan gwamnati da dama albashi

Sanatan da ke wakiltar Edo ta Arewa a Majalisar Dattawan Najeriya, Adams Oshiomole ya bayyana cewa naira 30,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi ta yi kaɗan.

Sanata Oshiomole ya bayyana hakan ne a hirarsa da gidan talabijin na Channels a ranar Lahadi.

Oshiomole ya ce N30,000 ta yi kaɗan a matsayin albashi
Adams Oshiomole ya ce N30,000 ta yi kaɗan a matsayin albashi, mai yi masa shara ma N60,000 yake ba ta. Hoto: Buharist Reporters
Asali: Facebook

Mai yi mun shara na samun naira 60,000

Oshiomole wanda kuma tsohon gwamnan jihar ta Edo ne, ya bayyana cewa mai yi masa share-share a gida ma naira 60,000 yake ba ta duk wata a matsayin albashi.

Kara karanta wannan

Tallafin Tinubu: “Rabon N8,000 Duk Yaudara Ce”, Gwamnan Kaduna Ya Fadi Dalili

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce kuma idan ace zai ɗauko wanda zai riƙa share masa gidansa, naira 60,000 ce mafi ƙarancin abinda zai iya ba shi.

Ya ce idan mutum ya canza naira 30,000 zuwa dalar Amurka a kan naira 800 ko naira 700 duk dala, zai fahimci cewa mafi ƙarancin alabashin da ake bayarwa sakarcin banza ne kawai.

Oshiomole ya ce ma'aikatan kamfanoni sun fi ma'aikatan gwamnati albashi

Oshiomole ya kuma bayyana cewa mafi yawa daga ma'aikatan kamfanoni masu zaman kansu sun fi da yawa daga ma'aikatan Gwamnatin Tarayya da na jihohi albashi mai kyau.

Ya ce yana tunanin matar da ke share masa gida ko kwalin firamare ma ba ta da shi, amma tunda ta san yadda zata share masa gida, yana biyanta aƙalla naira 60,000 ne a matsayin albashi.

Ya ƙara da cewa ba zai iya ba ta ƙasa da naira 60,000 ba, saboda bai san iya ɗawainiyar da take a kanta ba kamar yadda Vanguard ta wallafa.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa Ya Bankaɗo Badaƙalar Maƙudan Kuɗi, Ya Ceto Biliyan N1.2 Daga Ma'aikata

Oshiomole ya kuma ce mai yi masa share-share a gidan nasa ta taɓa faɗa masa cewa yara huɗu gareta, wanda da wannan albashin da yake ba ta take kula da su.

Sannan ya ce duk da haka ba shi da tabbacin cewa waɗannan kuɗaɗen da yake ba ta ma za su isheta gudanar da kalar rayuwar da take so.

NULGE ta bayyana jerin gwamnonin da ba sa iya biyan mafi ƙarancin albashi na N30,000

Legit.ng a baya ta yi rahoto cewa kungiyar ma'aikatan ƙananan hukumomi a Najeriya (NULGE), ta koka kan yadda wasu gwamnoni suka gagara biyan naira 30,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi a jihohinsu.

Kungiyar ta kuma nuna matuƙar takaicinta kan yadda jihar Zamfara ta gaza biyan ko da mafi ƙarancin albashi na naira 18,000 da aka sanya a baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel