Sanatoci 8 Daga PDP, NNPP, YPP Sun Tona Kulle-Kullen da Ake yi a Majalisar Dattawa

Sanatoci 8 Daga PDP, NNPP, YPP Sun Tona Kulle-Kullen da Ake yi a Majalisar Dattawa

  • An fara rikicin siyasa a kan wanda zai zama sabon shugaban marasa rinjaye a Majalisar Dattawa
  • A dalilin haka wasu Sanatoci su ka fitar da takarda cewa jam’iyyar APC na neman yi masu karfi da yaji
  • ‘Yan majalisar sun sha alwashi ba za su bari wasu dabam su dauko wanda zai zama shugabansu ba

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Wasu Sanatoci takwas daga jam’iyyun hamayya sun ankarar da al’umma cewa su na zargin ana neman a kakaba masu shugaban marasa rinjaye.

A wani jawabi da su ka fitar a ranar Asabar, Premium Times ta ce Sanatocin sun tuhumi wasu da neman kawo masu rudani a zauren majalisar dattawa.

Kamar yadda ‘yan majalisar su ka bayyana, akwai wasu daga ciki da wajen majalisar tarayya da su ke neman raba kan ‘yan adawa da nufin a rage masu kafi.

Kara karanta wannan

Innalillahi: 'Yan Ta'adda Sun Kashe Basarake Bisa Kuskure, Sun Sace Mutum 3 a Wata Jihar Arewa

Majalisar dattawa
Sanatoci a Majalisar Dattawa Hoto: @NgrSenate
Asali: Facebook

Sanatocin da su ka sa-hannu a wannan jawabin da aka fitar sun fito ne daga jihohi dama da su ka hada da Sokoto, Bayelsa, Bauchi, Benuwai da Anambra.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sannan akwai Sanatocin mazabun Kebbi, Imo da Kano cikin wadanda su ke korafin.

Karfa-karfa a Majalisar Tarayya

‘Yan jam’iyyar adawar da su ka fito daga PDP, NNPP da LP sun shaida cewa ana so ayi amfani da karfi, a nada masu shugabanin da sam ba su gamsu da su ba.

Legit.ng Hausa ta fahimci babu wani Sanata daga jam’iyyar hamayya ta LP a cikin Sanatocin da su ka sa hannu a wannan takardar korafi da aka fitar a jiya.

Takardar ‘yan majalisar ta ja hankalin al’umma cewa Sanatocin jam’iyyun hamayya ba su cin ma matsaya kan wanda zai zama shugaban marasa rinjaye ba.

Kara karanta wannan

Hukumar DSS Ta Tona Shirin ‘Yan Ta’adda a Lokacin Bukukuwan Sallah a Najeriya

Su wane Sanatoci ne korafi?

Sanatocin sun hada da: Mohammed Aliero (PDP, Kebbi); Seriake Dickson (PDP, Bayelsa); Aminu Tambuwal (PDP, Sokoto) da Abdul Ningi (PDP, Bauchi).

Sauran 'yan majalisar su ne: Abba Moro (PDP, Benuwai); Ezenwa Onyewuchi (PDP, Imo); Sumaila Kawu (NNPP, Kano), sai Ifeanyi Ubah (YPP, Anambra).

The Cable ta ce Sanatocin nan na ganin jam’iyya mai-ci na neman murkushe ‘yan adawa, su ka ce ba za a yi nasara ba, dole su taka masu burki a kasar.

Sabanin NNPCL v FAAC

An ji labari wasu sun fadawa Shugaban kasa abubuwa da-dama tun da ya shiga ofis game da NNPC Limited, ganin kamfanin bai kawo sisi a asusun FAAC.

Shugabannin kamfanin sun rubutawa Bola Tinubu takarda domin agano meyasa kudi ba su shiga asusun tarayyar kuma shugaban Najeriyan ya amince.

Asali: Legit.ng

Online view pixel