"Bai Kamata Tinubu Ya Iya Dakatar Da Emefiele Ba": Fitaccen Lauya Ya Bayyana

"Bai Kamata Tinubu Ya Iya Dakatar Da Emefiele Ba": Fitaccen Lauya Ya Bayyana

  • Mutane da dama sun tofa albarkacin bakinsu bayan dakatarwar da Shugaba Bola Tinubu ya yi wa gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele
  • Masu amfani da yanar gizo, ciki har da lauyoyi a dandalin sada zumunta na Tuwita, sun bayyana ra’ayoyi daban-daban kan dakatarwar
  • Shahararren lauya Inibehe Effiong, ya yi kira da a yi taka tsan-tsan kan lamarin yayin da yake kafa hujjoji da abinda doka ta tanada

FCT, Abuja – Lauya mai zaman kansa, Inibehe Effiong, ya ce bai kamata shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya iya dakatar da gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele ba.

Effiong ya bayyana hakan ne a yayin da yake mayar da martani, dangane da dakatarwar da Shugaba Bola Tinubu ya yi wa Godwin Emefiele a ranar Juma’a, 9 ga watan Yuni.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: DSS Ta Yi Martani Kan Zargin Kama Gwamnan CBN

Abinda ya sa Tinubu ba zai iya dakatar da Emefiele ba
Fitaccen lauya ya ce doka ba ta ba Tinubu damar dakatar da Emefiele ba. Hoto: Inibehe Effiong, Central Bank of Nigeria, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Dokar CBN ba ta ba wa shugaban ƙasa damar dakatar da gwamnan ba, cewar Effiong

Effiong ya bayyana cewa duba da cewa CBN na da ‘yancin cin gashin kansa, bai kamata ace Shugaba Tinubu ya samu ikon dakatar da shugaban babban bankin shi kaɗai ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Effiong ya wallafa ra'ayin nasa ne a ranar Juma'a, 9 ga watan Yuni, a shafinsa na Tuwita. Ga abinda yake cewa:

"Godwin Emefiele ya lalata CBN tare da yin shirme game da farashin kuɗinmu a kasuwar hada-hadar kuɗi."
"Duk da haka, Tinubu ba zai iya tsige shi ba bisa ga sashe na 11 na dokar CBN ba tare da neman izinin majalisar dattawa ba."
“Ra’ayina shi ne, tun da dokar CBN ba ta ba wa shugaban ƙasa damar dakatar da gwamnan ba, kuma idan aka yi la’akari da cewa CBN na da ‘yancin cin gashin kai wanda ba za a iya tabbatar da shi ba tare da mutunta wa’adin gwamnan ba, bai kamata a ce shugaban ƙasa ya iya dakatar da shi ba."

Kara karanta wannan

Bola Tinubu Da Emefiele: Abubuwa 4 Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Dakatar Da Gwamnan CBN

"Wannan ra'ayi na ne na kaina kuma yana ƙarƙashin hukuncin babbar kotun tarayya (a shari'ar Sanusi Lamido da aka yi."

Emefiele bai cancanci shugabantar CBN ba

Bugu da kari, lauyan ya kuma bayyana cewa ce shi baya ganin Emefiele a matsayin wanda ya cancanci ya jagoranci babban bankin Najeriya.

Ya ƙara da cewa ya kamata gwamnan na CBN da aka dakatar, ya yi bayani a kan yadda ya gudanar da ayyukansa, kuma a tuhume shi kan dukanin munanan ayyukan da ake zargin ya aikata.

Emefiele ba ya hannunmu, cewar DSS

A wani rahoto da Legit.ng ta wallafa, Hukumar tsaro na farin kaya (DSS), ta bayyana cewa Godwin Emefiele, gwamnan CBN da aka dakatar, ba ya a hannunsu.

Hukumar ta DSS ta fitar da sanarwar ne a shafinta na Tuwita, biyo bayan raɗe-raɗin da ake ta yi na cewar sun kama Emefiele bayan dakatar da shi da Shugaba Tinubu ya yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel