Daga Karshe, PDP Ta Zabi Sabon Shugaban Jam'iyya a Jihar Osun

Daga Karshe, PDP Ta Zabi Sabon Shugaban Jam'iyya a Jihar Osun

  • Jam'iyyar PDP ta gudanar da gangamin taron zaben shugabanni a matakin jihar Osun ranar Laraba 3 ga watan Mayu
  • Bayan Deleget sun kammala kaɗa kuri'a, PDP ta bayyana sabon shugaban jam'iyya, Sakatare da sauransu
  • Wannan dai na zuwa ne makonni bayan Kotun jihar Osun ta halasta tarukan da PDP ta gudanar a matakai biyu

Osun - Tsohon shugaban jam'iyyar Peoples Democratic party (PDP) na rikon kwarya a jihar Osun, Sunday Bisi, ya zama zababben shugaban jam'iyya reshen jihar.

Channels tv ta tattaro cewa an ayyana Mista Bisi a matsayin sabon shugaban PDP na jihar Osun da kuma Bola Ajao, wansa ya ɗare kujerar Sakataren jam'iyyar bayan kaɗa kuri'a ranar Laraba.

Sabon shugaban PDP a Osun.
Daga Karshe, PDP Ta Zabi Sabon Shugaban Jam'iyya a Jihar Osun Hoto: Hon. Adewumi Adeyemi
Asali: Facebook

A ranar Laraba (Jiya) 3 ga watan Mayu, 2023, jam'iyyar PDP ta gudanar da gangamin taron zaɓen shugabanni a filin wasan Osogbo, babban birnin jihar Osun.

Kara karanta wannan

"Ba Ka Bi Na Bashin Komai": Wasu Muhimman Abubuwa 5 Da Tinubu Ya Fada Yayin Da Wike Ya Gayyace Shi

Deleget uku daga kowace gunduma a kananan hukumomin jihar ne suka kaɗa kuri'a a wurin gangamin taron.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mista Bisi ya sha alwashin goyon bayan gwamna Adeleke

A jawabin godiya bayan samun nasara, sabon shugaban jam'iyyar ya ce wa'adin mulkinsa zai maida hankali wajen karfafa haɗin kai da jawo kowane mamba a jiki.

Haka nan ya ƙara da cewa zai haɗa alaka mai danƙo da gwamna Ademola Adeleke domin tabbatar da manufofinsa ga jihar Osun sun zama gaskiya, kamar yadda Dailypost ta ruwaito.

Gwamna Adeleke ya bukaci haɗa kai wuri ɗaya

A nasa jawabin, gwamna Adeleke ya yi kara ga baki ɗaya mambobin PDP da su haɗa kansu su zama tsinstiya guda, su baiwa sabbin shugabanni goyon bayan da ya kamata.

A kwanakin baya idan baku manta ba, babbar kotun jihar Osun ta yanke cewa tarukan da PDP ta gudanar a matakin gunduma da kananan hukumomi halastattu ne.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Matashin Saurayi Ya Burma Wa Mahaifiyarsa Wuƙa Har Ta Mutu a Kano

A wani labarin kuma Yakubu Gowon Ya Roki Yan Najeriya Su Rungumi Hukuncin da Kotu Zata Yanke Kan Zaben 2023

Tsohon shugaban ƙasa a mulkin soja, Janar Yakubu Gowon, ya buƙaci yan Najeriya su aminta da duk hukuncin da Kotu zata yanke nan gaba kan babban zaben 2023.

Gowon ya kuma nemi kowa ya kama bakinsa ya yi shiru, a bar Kotu ta yi aikinta ba tare da katsalandan ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel