Da Dumi-Dumi: Gwamnan PDP Ya Rushe Kwamishinoni Da Hadimansa Daga Mukaman Su

Da Dumi-Dumi: Gwamnan PDP Ya Rushe Kwamishinoni Da Hadimansa Daga Mukaman Su

  • Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya yi tankaɗe da rairayi a majalisar zartarwar jihar
  • Gwamnan ya rushe ilahirin majalisar zartarwar jihar gabaɗayan ta, wacce ta ƙunshi kwamishinoni da wasu na kusa da gwamna
  • Gwamna Obaseki bai sanar da dalilin sa ba na sallamar su daga muƙaman su ba a cikin sanarwar sallamar su da ya fitar

Jihar Edo - Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ya rushe majalisar zartarwar jihar gabaɗayan ta.

Gwamnan ya ɗauki matakin rushe majalisar zartarwar ne a ranar Laraba, 3 ga watan Mayun 2023, rahoton Tribune ya tabbatar.

Gwamnan jihar Edo ya kori kwamishinonin sa
Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki Hoto: Vanguard.com
Asali: UGC

Majalisar zartarwar ta ƙunshi kwamishinoni, masu bayar da shawara na musamman da manyan hadiman gwamna.

Gwamna Obaseki ya bayyana cewa rushe su da ya yi daga kan muƙaman su, za ta fara aiki ne nan take.

Kara karanta wannan

Mai Neman Shugabancin Majalisar Dattawa Ya Kebe Da Shugaba Buhari, Ya Bayyana Yankin Da Ya Cancanci Kujerar

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamnan ya sanar da rushe majalisar zartarwar ne a wajen taron mako-mako da aka gudanar na majalisar a ranar Laraba, 3 ga watan Mayun 2023.

Obaseki ya nuna godiyar sa a gare su bisa aikin da suka yi wa gwamnatin jihar da al'ummar jihar baki ɗaya, cewar rahoton Independent.

A wata sanarwa da Crusoe Osagie, ya fitar, dukkanin wasu masu riƙe da muƙamin siyasa, da suka haɗa da hadiman gwamnan, da masu bayar da shawara na musamman, duk an sallame su daga muƙaman su.

Sanarwar dai ba ta yi ƙarin haske ba kan dalilan da ya sanya gwamnan ya sallame su daga kan muƙaman su ba.

Shugaba Buhari Ya Bayyana Wani Muhimmin Alkawari Da Ya Cikawa 'Yan Najeriya

A wani rahoton na daban kuma, kun ji yadda shugaban ƙasan Najeriya mai barin gado, Muhammadu Buhari, ya bugi ƙirjin cewa ya cikawa ƴan Najeriya alƙawarin da ya ɗaukar mu su.

Kara karanta wannan

Shugaban Hukumar Tsaro a Jihar Arewa Ya Tsallake Rijiya Da Baya a Hannun 'Yan Bindiga, Cikakkun Bayanai Sun Bayyana

Shugaban ƙasar ya kuma ce gwamnatinsa, sai dai son barka domin ta tsamo dubunnan ƴan Najeriya daga cikin ƙangin talaucin da ya yi mu su katutu. Shugaba Buhari ya ce yanzu ƴan Najeriya sai dai son barka.

Muhammadu Buhari ya yi wannan furucin ne a birnun tarayya Abuja, lokacin da ya je ƙaddamar da wani ƙatafaren aiki da gwamnatinsa ta aiwatar a birnin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel