Shugaban Hukumar Yaki Da Dabanci a Jihar Zamfara Ya Sha Da Kyar a Hannun 'Yan Bindiga

Shugaban Hukumar Yaki Da Dabanci a Jihar Zamfara Ya Sha Da Kyar a Hannun 'Yan Bindiga

  • Kwamandan rundunar yaƙi da dabanci jihar Zamfara ya sha da kyar a hannun wasu ƴan bindiga
  • Bello Bakyasuwa ya bayyana cewa sun yi musayar wuta da ƴan bindigan kafin ƴan sanda su kawo masa ɗauki
  • Ƙwamandan ya yi kira ga jami'an tsaro da su kawo masa ɗauki domin rayuwars na cikin haɗari

Jihar Zamfara - Kwamandan hukumar yaƙi da dabanci ta jihar Zamfara, Bello Bakyasuwa, ya tsallake rijiya da baya a wani mummunan hari da ƴan bindiga suka kai masa yana kan hanyar sa ta zuwa Kaduna daga birnin Gusau.

A wata sanarwa da ya rabawa manema labarai ranar Talata, Bakyasuwa ya ce wasu mutane ɗauke da manyan bindigu sun kai masa hari kan titin hanyar Funtua-Zaria, da yammacin ranar Alhamis.

Shugaban hukumar yaki da dabanci a Zamfara, ya sha da kyar a hannun 'yan bindiga
Bello Bakyasuwa, shugaban hukumar yaki da dabanci ta jihar Zamfara Hoto: Analyzernews.com
Asali: UGC

Channels tv ta rahoto Bakyasuwa, wanda tsohon soja ne na cewa:

Kara karanta wannan

Halin da Wasu Ɗaliban Najeriya Suka Shiga Bayan Motar da Ta Kwaso Su Daga Sudan Ta Kama da Wuta

"Na tsallake mutuwa kwana huɗu da suka wuce akan hanyata ta zuwa Kaduna, a wajen hanyar Funtua-Zaria. Yanzu haka ina kwance a asibiti, rayuwata na cikin haɗari, ina fuskantar hare-hare daga ƴan bindigan da na ke tunanin hayar su aka yi."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bakyasuwa ya yi nuni da cewa lokacin da ya bar Gusau zuwa Kaduna a motar Hilux ɗin sa, ya lura da wasu motocin Hilux guda 2 da wata BMW na biye da shi a baya.

"Na kasa samun sukuni da motocin suke biye da ni, a dalilin haka sai na tsaya a shingen binciken jami'an tsaro na Yankara, sai motocin suka wuce ni."
"Na cigaba da tafiya ta sannan bayan na wuce Funtua da wajen misalin ƙarfe 8:30 na dare, sai na lura motocin Hilux ɗin da BMW sun cigaba da biyo ni, inda motar BMW ɗin ta sha gabana ta sanya na dakata don dole akan titi."

Kara karanta wannan

Shugaban Majalisar Dattawa Ya Ja Hankalin Atiku da Obi, Ya Faɗi Abinda Ya Rage Musu Kan Zaben 2023

"Mutanen da ke cikin motocin kawai sai suka buɗewa motata wuta inda muka kwashe wasu ƴan mintuna muna musayar wuta da su. Na yo tsalle na fito daga motata wanda a dalilin hakan na karye a ƙafa sannan na samu raunika a fuska ta."
"Amma makasan waɗanda hayar su aka ɗauko, sun cigaba da harbi, na samu da. kyar na tsira zuwa cikin daji, yayin da jini ya ke ta zuba daga jikina."

Ya ce ya taki sa'a ƴan sanda sun ceto shi, waɗanda suka ƙaraso wajen bayan sun ji harbe-harben bindiga, cewar rahoton Daily Post.

"Lokacin da ƴan sanda suka iso wajen, sun ceto ni cikin gaggawa sannan suka kai ni wani ƙaramin asibiti da ke kusa da wajen." A cewarsa
"Bayan an gama duba ni a asibitin, na kwana a ƙauyen, inda da safe direba na da ya zo ya sameni a ƙauyen, ya wuce da ni zuwa Kaduna domin cigaba da duba lafiyata."

Kara karanta wannan

Bayin Allah Da Dama Sun Jikkata, Dukiyoyi Sun Salwanta a Wani Mummunan Fada Da Ya Barke a Jihar Arewa

Bakyasuwa ya ce motar Hilux ɗin sa ta yi kaca-kaca a dalilin ruwan harsasan da aka yi mata.

Ya kira ga hukumomin tsaro da kawo masa agaji, inda ya ƙara da cewa rayuwar sa tana cikin haɗari.

Tashin Hankali Yayin Da Dalibar 400L a Uniben Ta Mutu Tana Cikin Barci

A wani rahoton na daban kuma, kun ji cewa wata ɗalibar jami'a ta koma ga mahaliccinta, tana cikin barci.

Ɗalibar dai tana ajin ƙarshe ne a jami'ar Benin, da ke a birnin Benin na jihar Edo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel