Mai Neman Shugabancin Majalisar Dattawa Ya Kebe Da Shugaba Buhari, Ya Bayyana Yankin Da Ya Cancanci Kujerar

Mai Neman Shugabancin Majalisar Dattawa Ya Kebe Da Shugaba Buhari, Ya Bayyana Yankin Da Ya Cancanci Kujerar

  • Gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi ya sanya labule da shugaba Buhari a fadar da da ke Villa Abuja
  • Gwamnan a ya yin ziyarar ta sa, ya gayawa shugaba Buhari aniyar sa ta son zama shugaban majalisar dattawa
  • Umahi ya yi nuni da cewa babu yankin da ya cancanci samun wannan kujerar idan ba yankin Kudu maso Gabas ba

Abuja - Gwamna Dave Umahi na jihar Ebonyi kuma zaɓaɓɓen sanata yanzu. ya ziyarci shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, inda ya ce yankin Kudu maso Gabas, ya cancanci ya samu kujerar shugabancin majalisar dattawa..

Jaridar Vanguard tace, gwamna Umahi, a lokacin ganawar su, ya gayawa shugaba Buhari cewa yana da niyyar zama shugaban majalisar dattawan.

Gwamna Umahi ya ziyarci shugaba Buhari
Shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da gwamna Dave Umahi, na jihar Ebonyi Hoto: Buhari Sallau
Asali: Twitter

Gwamnan ya bayyana cewa yankin Kudu maso Gabas, ya bayar da gudunmawa wajen samun nasarar zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Tinubu, sannan akwai buƙatar kowane yanki na ƙasar nan a tafi tare da shi, cewar The Cable.

Kara karanta wannan

Daga Karshe Gaskiya Ta Bayyana Dangane Da Batun Sanya Labulen Peter Obi Da Bola Tinubu

Ya gargaɗi jam'iyyar All Progressives Congress (APC), kan zaɓar ƴan takarar ta akan yawan ƙuri'u da yankin su ya ba jam'iyyar, inda ya buƙace ta da ta yi gaskiya da adalci, wajen raba muƙaman majalisar ta 10.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da ya ke magana da ƴan jaridan fadar shugaban ƙasa bayan kammala ganawar sa da shugaba Buhari, Umahi ya bayyana cewa:

"Idan ka ce yankin Kudu maso Gabas, bai yi wa APC ruwan ƙuri'u ba, a ƙalla yankin ya kare cewa APC ba ayi mata rata sosai ba. Hakan yana da matuƙar muhimmanci."
"Idan aka yi duba kan haƙiƙanin yadda al'ummar mu su ke, za ku yarda da ni cewa abinda yakamata shugabanni su yi ba tare da sun nuna bambanci ba shine yankin Kudu maso Gabas, ya cancanci samun kujera mafi tsoka ta uku a ƙasar nan. Hakan yana da matuƙar muhimmanci."

Kara karanta wannan

Zabin Tinubu a Shugabancin Majalisar Dattawa Ya Yi Kus-Kus da Shugaba Buhari, Bayanai Sun Bayyana

"Na sha faɗin cewa za ka iya ɗaukar wani saboda dalilin yawan ƙuri'u na wani yanki, amma kana buƙatar haɗin kan ƴan tsirarun domin samun ƙasa mai zaman lafiya da za ka mulka. Hakan yana da matuƙar muhimmanci."
"Don haka, saboda a tafi da kowa domin haɗin kan ƙasa, domin a ba kowa dama, babu wanda ya ce wannan shine dalilin da ya sanya bai kamata a ba yankin Kudu maso Gabas wannan muƙamin ba."

Zabin Tinubu a Shugabancin Majalisar Dattawa Ya Yi Kus-Kus da Shugaba Buhari

A wani rahoton kuma, kun ji cewa wanda Tinubu ya ke so ya shugabanci majalisar dattawa ta 10, ya sanya labule da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.

Sanata Godswill Akpabio, ya ziyarci shugaba Buhari ne domin ƙara jaddada aniyar sa ta neman shugabancin majalisar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel