Hadimin Atiku Ya Yi Hasashen Mutum 20 da Bola Tinubu Zai Ba Mukamai a Gwamnati

Hadimin Atiku Ya Yi Hasashen Mutum 20 da Bola Tinubu Zai Ba Mukamai a Gwamnati

  • Daniel Bwala ya fadi wasu da yake kyautata zaton Bola Tinubu zai ba su mukamai a gwamnatinsa
  • A wani hasashe da ya yi a Twitter, Mai magana da bakin Atiku Abubakar ya raba Ministoci goma
  • Bwala ya fadi wanda zai zama SGF, NSA, Shugaban ma’aikatan fada, da mai magana da bakin Tinubu

Abuja - Daniel Bwala wanda Mai magana da yawun bakin Atiku Abubakar ne a zaben 2023, ya yi hasashen yadda Gwamnatin mai zuwa za ta kasance.

A ranar Juma’a, Daniel Bwala ya rika jero wasu ‘yan siyasa da kuma mukaman da yake ganin za su samu idan Bola Ahmed Tinubu ya hau karagar mulki.

Tsohon jagoran na jam’iyyar APC mai mulki ya yi hasashen wadanda za su zama Ministoci, Hadiman shugaban Najeriya da kuma shugabannin majalisa.

Kara karanta wannan

Shugaban Majalisar Dattawa Ya Ja Hankalin Atiku da Obi, Ya Faɗi Abinda Ya Rage Musu Kan Zaben 2023

Kamar yadda Vanguard ta bibiyi ‘dan siyasar a shafinsa, ga yadda ya yi hasashen na shi:

Jerin shugabannin gobe

Shugaban kasa - Bola Ahmed Tinubu

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Mataimakin shugaban kasa - Kashim Shetima

Shugaban majalisar dattawa - Godswill Akpabio

Tinubu
Bola Tinubu da Gwamnonin APC Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Twitter

Shugaban ma’aikatan fada - Femi Gbajabiamila

Mai bada shawara kan tsaro - Nuhu Ribadu

Hadimin harkar cikin gida - Babajimi Benson

Sakataren gwamnatin kasa - Nasir El-Rufai

Mai magana da yawu - Festus Kayamo

Ministan harkar musamman - James Faleke

Ministan birinin Abuja - Yahaya Bello

Ministan tsaro - Tukur Buratai

Ministan yada labarai - Bayo Ononuga

Ministan harkokin waje - Kayode Fayemi

Ministan cikin gida - Nyesom Wike

Ministan shari’a (AGF) - Babatunde Fashola

Ministan harkar noma - Ben Ayade

Ministan jiragen sama - Femi Fani Kayode

Ministan ayyuka - Ken Nnamani

Lauyan gidan gwamnati - Babatunde Ogala

Rahoton Daily Post ya nuna Bwala ya hango Dele Alake a kujerar Jakadan Najeriya a Amurka, amma bai san shugaban majalisar wakilai ba.

A cewarsa, Buba Marwa zai cigaba da rike NDLEA, sai Wale Edun ya zama Gwamnan babban banki, ya yi gum a kan kujerun EFCC, DSS da NIA.

Kara karanta wannan

Gwamnonin PDP 2 Sun Gana da Tinubu a Abuja, Gwamna Wike Ya Yi Magana Mai Jan Hankali

Buhari da Gwamnoni

Da ya hadu da kungiyar PGF, an ji labari Mai girma Muhammadu Buhari ya ware Gwamnonin Kano da Kaduna, ya yaba masu kan cigaban da suka kawo.

A wajen ne aka ji Sugaba Buhari ya ce Atiku Abubakar da Peter Obi sun hango kansu a mulki, har sun fara tunanin daula, amma Bola Tinubu ya doke su a zabe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel