Jerin Gwarazan Matan Arewacin Najeriya 7 da Suka yi Suna a Fagen Siyasa Kafin Binani

Jerin Gwarazan Matan Arewacin Najeriya 7 da Suka yi Suna a Fagen Siyasa Kafin Binani

Abuja - Rahotonmu ya tattaro mata da suka yi suna a fagen siyasa, musamman wadanda suka yi takara, suka samu nasara a zabe ko suka rike mukamai.

Baya ga su akwai fitattun ‘yan siyasa daga Arewacin Najeriya wadanda mata ne, misali; Naja’atu Mohammed, Baraka Sani, Saudatu Sani, da Hadiza Sabuwa.

A tarihi an yi irinsu Gambo Sawaba wanda tayi gwagwarmaya domin ceto marasa karfi.

A ‘yan baya-bayan nan, an samu Natasha Akpoti wanda ta shiga takara a jihar Kogi, duk da ba tayi nasara ba, ta rika girgiza duk mazan da suka gwabza da ita.

1. Gbemisola Ruqayyah Saraki

A 2003 Gbemisola Ruqayyah Saraki ta zama Sanata mai wakiltar Kwara ta tsakiya ta na shekara 38. Yanzu haka itace karamar Ministar sufuri a gwamnatin tarayya.

Gbemisola Saraki wanda tayi karatu a Ingila ta gaji mahaifinta, Olusola Saraki a siyasa.

Kara karanta wannan

Shawarar da Gwamnoni Suka Ba Tinubu Tana Neman Jawo Yaki a Majalisar Tarayya

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

2. Nenadi Esther Usman

Nenadi Esther Usman ta rike Sanatar kudancin Kaduna a majalisar dattawa, sannan ta zama Minista ba sau daya ba a lokacin Olusegun Obasanjo yana kan mulki.

Nenedi ta wakilci Kachia/Kagarko a majalisa a 1998 kafin zama Ministar kudi.

3. Sadiya Farouq

A lokacin da aka kafa jam’iyyar CPC, Sadiya Umar Farouk ce ta zama Ma’ajiya ta kasa, bayan an kafa gwamnati a Jam’iyyar APC a 2015, aka cigaba da damawa ita.

Sadiya Farouq mai shekara 48 ta na rike da kujerar Ministar jin kai da bada agajin gaggawa.

Aisha Binani
SGF, Binani, Buhari, Adamu a Aso Rock Hoto: sunnewsonline.com
Asali: Twitter

4. Zainab Kure

A 1999, Zainab Kure ta zama uwargidar jihar Neja da Mai gidanta Abdulkadir Kure ya zama Gwamna. A Yunin 2007 ta zama cikin matan da suke majalisar dattawa.

Kafin Kure ta zama Sanatar Neja ta Kudu, ta kai matsayin Sakatariyar din-din-din a gwamnati, a 2018 ta jagorancin yakin neman shugaban kasa na David Mark a PDP.

Kara karanta wannan

Hukuncin Addinin Musulunci Idan Bikin Idi Ya Hadu da Sallar Juma'a a Rana Daya

5. Binta Masi Garba

Sai da Binta Masi Garba ta lashe zabe sau uku a majalisar tarayya tsakanin 1999 da 2011 ta na wakiltar Kaduna ta Kudu da kuma Madagali/Michika a karkashin PDP.

Daga baya ta zama Sanata a mahaifarta, kafin nan ta rike shugabar APC a Adamawa.

6. Aisha Jummai Alhassan

Aisha Jummai Al-Hassan ta fi shahara da Mama Taraba, ita ce macen farko da ta zama Kwamishinar shari’a a Taraba, kafin ta tafi majalisar dattawa a 2007.

Mama Taraba ta doke Gwamna mai-ci a zaben Sanata, sannan tayi takarar Gwamna sau biyu amma ba ta kai labari ba, tsakanin nan, tayi Ministar harkar mata.

7. Aisha Dahiru Binani

Kamar Binta Garba, Aisha Binani ta wakilci mazabarta a majalisar wakilan tarayya, daga baya ta canji Abdulaziz Nyako wajen zama Sanatar Adamawa ta tsakiya.

A 2023, Sanata Binani ta doke Nuhu Ribadu wajen samun takarar Gwamna a APC.

Rikici ya shigo PDP

Kara karanta wannan

Ba da Mace Nayi Takara ba – Fintiri ya Fadi Asalin Abokan Gwabzawarsa Bayan Ya Zarce

Ana da labari cewa tsohon Mataimakin Gwamna da wasu ‘yan takara sun kalubalanci nasarar Dino Melaye wajen zama 'dan takaran PDP a Kogi.

An ce Sanata Melaye ya bada cin hanci a zaben tsaida ‘dan takara domin samun tikitin Gwamna, da aka tambaye shi kan zargin, sai ya yi ta kame-kame.

Asali: Legit.ng

Online view pixel