PDP Ta Jingine Wike, Makinde da Wasu Gwamnoni, Ta Naɗa Adeleke a Babban Muƙami

PDP Ta Jingine Wike, Makinde da Wasu Gwamnoni, Ta Naɗa Adeleke a Babban Muƙami

  • Jam'iyyar PDP ta yi watsi da gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas da sauran gwamnonin G-5 da suka juya mata baya a zaben shugaban kasa
  • Hakan ta faru ne yayin da PDP ta sanar da Ademola Adeleke na jihar Osun da Kenneth Okon a matsayin shugabannin kwamitin zaɓe a Bayelsa da Imo
  • Sakataren tsare-tsaren PDP, Umar Bature, ya ce sun yi haka ne domin tabbatar da kudirin jam'iyyar na gudanar da sahihin zaɓen fidda gwani

Ga dukkan alamu jam'iyyar PDP ba ta yafe wa gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas, Seyi Makinde na jihar Oyo da sauran gwamnonin G-5 da suka ci amanarta ba.

Alamu sun nuna haka ne bayan jam'iyyar ta sanar da gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, a matsayin shugaban kwamitin shirya zaben fidda gwani a jihar Bayelsa.

Kara karanta wannan

Sanatan PDP Ya Ce Jam'iyyar Ta Cancanci Kayen Da Ta Sha a Zabe, Ya Bayar Da Dalilai

Wike, Makinde da Adeleke.
Gwamna Nyesom Wike, Seyi Makinde da Ademola Adeleke Hoto: Ademola Adeleke, Seyi Makinde
Asali: Twitter

Haka zalika a jihar Imo, babbar jam'iyyar hamayya ta sanar da sunan Honorabul Kenneth Okon a matsayin shugaban kwamitin zaɓe, kamar yadda jaridar Tribune ta rahoto.

Meyasa PDP ta naɗa Adeleke a matsayin shugaban kwamitin Bayelsa?

Wannan ci gaban na zuwa ne jim kaɗan bayan jam'iyyar ta fitar da jerin sunayen Deleget, waɗanda zasu zaɓi ɗan takarar gwamna a inuwar PDP a jihohin guda biyu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Umar Bature, Sakataren tsare-tsare na jam'iyyar PDP ta ƙasa ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin 10 ga watan Afrilu.

Ya ce jam'iyyar ta ɗauki wannan matakin ne a yunƙurinta na tabbatar da an gudanar da sahihi kuma ingantaccen zaɓe, wanda kowa zai aminta da shi.

Kwamitin gudanarwa (NWC) ne ya amince da naɗin Adeleke da Okon, kuma su zasu jagoranci shirya zaɓen fidda ɗan takarar PDP a zaɓen gwamnan jihohin 2 da ke tafe.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: 'Yan Daba Sun Kutsa Kai Cikin Sakatariyar Jam'iyya Ta Ƙasa a Abuja

Gwamnonin G-5 ba su goyin bayan ɗan takarar shugaban kasa a inuwar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ba yayin zaɓen 25 ga watan Fabrairu, 2023 saboda rashin adalci a tsarin jam'iyya.

Buhari ya inganta tsaro a Najeriya - Adesina

A wani labarin kuma Fadar shugaban ƙasa ta bayyana yadda Buhari ya taka rawa wajen ƙara inganta tsaro a Najeriya bayan hawa mulki a 2015

Femi Adesina, kakakin shugaban kasa, ya ce maganar gaskiya Najeriya ta samu ci gaba a ɓangaren tsaro idan aka kwatanta da kafin zuwansa kan mulki.

Ya ce a baya yan ta'adda sun kwace iko da kananan hukumomi sama da 10 a arewacin Najeriya, amma yanzun komai ya dawo hannun gwamnati.

Asali: Legit.ng

Online view pixel