Rashin Tsaro: Buhari Zai Bar Najeriya Fiye da Yadda Ya Same Ta, Adesina

Rashin Tsaro: Buhari Zai Bar Najeriya Fiye da Yadda Ya Same Ta, Adesina

  • Fadar shugaban kasa ta yi ikirarin cewa tsaro ya inganta a Najeriya fiye da yadda Buhari ya same ta
  • Femi Adesina ya ce a baya akwai akalla kananan hukumomi 17 da ke ƙarƙashin 'yan ta'adda amma yanzun an kwato su
  • Ya ce idan aka kwatanta kafin zuwan Buhari da kuma bayan ya karbi mulki, yanayin tsaro ya inganta a Najeriya

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya taɓuka abin a zo a gani wajen daƙile kalubalen tsaro kala daban-daban a Najeriya tun da ya hau kan madafun iko a 2015.

Kakakin shugaban kasa, Femi Adesina, ne ya faɗi haka a cikin shirin Politics Today na Channels tv ranar Latinin, ya ce Buhari zai bar Najeriya fiye da yadda ya same ta.

Shugaba Buhari.
Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari Hoto: Buhari Sallau
Asali: UGC

Yayin da aka gaya masa sahihin bayani kan jumullar yan Najeriya 55,000 da aka kashe daga 2015 zuwa watan Mayu, 2022 a hannun yan ta'adda, yan bindiga da sauransu, Adesina ya ce Buhari ya inganta tsaro.

Kara karanta wannan

Fadar Shugaban Kasa Ta Bayyana Koma Bayan da Rashin Lafiyar Shugaba Buhari Ta Jawo a Najeriya

Mai magana da yawun shugaban kasan ya ce shugaba Muhammadu Buhari zai bar ɓangaren tsaron Najeriya da kyau fiye da yadda ya same shi bayan ya hau mulki a 2015.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A rahoton The Cable, Adesina ya ce:

"Adadin raguwa yake a hankali a hankali cikin shekarun nan kuma gaskiyar kenan ba wanda ya isa ya canja ta."

Haka zalika yayin da aka tambaye ko yanayin ƴa inganta, an samu ƙarin zaman lafiya a ƙasar nan lokacin Buhari, Adesina ya ce, "Sosai ma kuwa."

"A 2015, mun san halin da Najeriya take ciki, aƙalla kananan hukumomi 17 suna karkashin ikon 'yan ta'adda. Su ke juya komai, ina nufin sun kwace Masarautu, su ne a kujerar shugaban ƙaramar hukuma."
"Ba'a iya buɗe wurin baiwa matasa yan bautar ƙasa horo, bama a tura mutane can. Amma haka ke faruwa a yau? Ba haka bane, Sarakuna sun koma Masarautunsu Ciyamomi sun koma kujerunsu."

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: Yadda dan kasar waje ya shigo Najeriya da kayan hodar iblis a cikin kwaroron roba

"Yanzu ana buɗe wuraren baiwa matasa masu hidimtawa ƙasa horo kuma ana tura su aiki jihohin, duk da haka zaka ce mun ba'a samu ci gaba ba? Ba zai yuwu ba, mu faɗi gaskiya kawai."

Rashin Lafiyar Buhari Na Wata Takwas Ya Kawo Wa Mulkinsa Cikas, Adesina

A wani labarin kuma Fadar shugaban kasa ta bayyana koma bayan da aka samu sakamakon rashin lafiyar da Buhari ya yi tsawon watanni 8

Femi Adeshina, ya tuno yadda shugaba Muhammadu Buhari, ya kwashe kusan watanni 8 yana jinya a Landan a shekarar 2017.

Ya ce duk da ba abu ne mai daɗi ba amma sun ji daɗi lokacin da ya dawo da Najeriya da kwarinsa fiye da yadda ya tafi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel