Sanatan PDP Ya Ce Jam'iyyar Ta Cancanci Kayen Da Ta Sha a Zabe, Ya Bayar Da Dalilai

Sanatan PDP Ya Ce Jam'iyyar Ta Cancanci Kayen Da Ta Sha a Zabe, Ya Bayar Da Dalilai

  • Sanatan jami'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Ebonyi ya ce jam'iyyar ta cancanci kashin da ta sha a zaɓen gwamnan jihar
  • Sanata Obinna Ogba ya ce jam'iyyar ita ta janyo wa kanta rashin nasara a zaɓen gwamnan jihar
  • Ya kawo dalilansa sannan ya aike da wani muhimmin gargaɗi kan shugabannin jami'iyyar na ƙasa

Jihar Ebonyi- Sanata Obinna Ogba, sanata mai wakiltar Ebonyi ta tsakiya a majalisar dattawa, ya bayyana cewa jam'iyyar PDP ta cancanci shan kashi a jihar saboda yadda ƴan kwamitin gudunarwar ta na ƙasa suka yi rikon sakainar kashi da lamarinta.

Jaridar Premium Times ta rahoto cewa, Mr Ogba ya bayyana hakan ne yayin ganawa da manema labarai a mahaifarsa da ke Nkalagu cikin ƙaramar hukumar Ishielu a ranar Lahadi.

Obinna Ogba
Sanatan PDP Ya Ce Jam'iyyar Ta Cancanci Kashin Da Ta Sha a Zabe, Ya Bayar Da Dalilai Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Sanatan ya ce kwamitin gudanarwar jam'iyyar na ƙasa (NWC), shi ya janyo jam'iyyar ta samu matsala ta hanyar bayar da tikitin takarar gwamna ga ɗan takarar da bai dace ba.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Dumi: Bayan Dogon Lokaci, Gaskiyar Abinda Ya Sa Atiku Ya Sha Kaye a Zaben 2023 Ya Fito

Sanatan wanda ya rasa tikitin takarar gwamnan jihar bayan an kwashe dogon lokaci ana shari'a a kotu, inda daga ƙarshe kotun koli ta raba gardama, ya gargaɗi NWC da kada su kuskura su dakatar da wani mamba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A kalamansa:

"Maganar gaskiya itace mambobin NWC ne suka cancanci a dakatar da su tun daga kan shugaban jam'iyyar na ƙasa.
“Shugaban jam'iyya na ƙasa ya kasa kawo akwatin zaɓensa, mazaɓarsa, ƙaramar hukumarsa da jiharsa, haka abin ya kasance ga dukkanin waɗanda aka haɗa baki da su aka ba wadanda suka fahimci yarensu tikitin takara."

Sai dai, Mr Ogba ya ƙara da cewa har hanzu akwai sauran fata ga jam'iyyar PDP saboda mutane na son ta.

“Abinda muke buƙata shine shugabannin da suka dace waɗanda zasu gudanar da lamuran jami'iyyar saboba babu jam'iyyar da ke da ƙarfi kamar PDP."

Kara karanta wannan

An samu matsala: Jam'iyyar APC ta kori wani fitaccen sanata a jihar Arewa

Shugabannin PDP sun ci dunduniyar jam'iyyar a jihar

Ya kuma yi nuni da cewa shugabannin jami'iyyar PDP a jihar sun marawa ɗan takarar gwamnan jam'iyyar APC a jihar baya saboda gaskiya da adalci domin raba mulki zuwa kowane yanki na jihar, rahoton Peoples Gazette.

A cewarsa:

“Jam'iyyun siyasa matakala ce kawai ta samun muƙaman siyasa daban-daban.
“Shugabannin PDP a Ebonyi sun sanya mun yi amanna cewa yankin Arewacin jihar nan ya kamata su samar da gwamna, sannan ina farin ciki cewa waɗanda na marawa baya sun samu nasara a zaɓen su."

Jam’iyyar da ta Goyi Bayan Tinubu, Ta Kai Shi Kotu

A wani labarin na daban kuma, wata jam'iyya ta shiga cikin jerin jam'iyyun da ke ƙalubalantar nasarar da Tinubu ya samu a zaɓen shugaban.

Jami'iyyar wacce a da ta mara masa baya tana zargin anyi murɗiyar zaɓe a jihohi 11.

Asali: Legit.ng

Online view pixel