Ana Saura Kwanaki 50 Ya Bar Aso Rock, An Yi Karar Shugaba Buhari da NBC a Kotu

Ana Saura Kwanaki 50 Ya Bar Aso Rock, An Yi Karar Shugaba Buhari da NBC a Kotu

  • SERAP da CJID sun tanadi Lauyoyi da suka shigar da karar Shugaban Najeriya a gaban kotu
  • Kungiyoyin masu zaman kan su sun kalubalanci tarar da hukumar NBC ta ci tashar Channels TV
  • Hirar da aka yi da Yusuf Datti Baba Ahmed ta jefa gidan talabijin a matsala, za su biya tarar N5m

Abuja - Kungiyar nan ta SERAP da CJID da aka kafa domin cigaban aikin jarida ta shigar da kara a kan shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.

Dalilin zuwa kotun shi ne tarar Naira miliyan biyar da gwamnatin tarayya ta laftawa tashar talabijin Channels, The Cable ta fitar da wannan rahoto.

Kungiyoyin sun hada da hukumar NBC da Ministan labarai da al’adu, Lai Mohammed a karar mai lamba FHC/L/CS/616/2023 a kotun tarayya na Legas.

Hakan na zuwa ne bayan NBC ta ci tarar tashar yada labaran a sanadiyyar wata hira da aka yi da Yusuf Datti Baba Ahmed inda aka ce ya saba doka.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: Yadda dan kasar waje ya shigo Najeriya da kayan hodar iblis a cikin kwaroron roba

Datti Baba Ahmed ya jawo aiki

Datti Baba Ahmed ya fito gaban talabijin yana mai cewa Bola Tinubu bai cika sharudan da za a rantsar da shi a matsayin shugaban kasa ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lauyoyin da suka shigar da kara a madadin SERAP da CJID sun hada da Kolawole Oluwadare, Andrew Nwankwo sai kuma Blessing Ogwuche.

Shugaba Buhari
Shugaban kasa Muhammadu Buhari a masallaci Hoto: @BuhariSallauOnline
Asali: Facebook

Lauyoyin suke cewa matakin da hukumarta dauka ya sabawa doka da kundin tsarin mulki, suka ce tarar ta saba sashe na 22, 36 da 39 na tsarin mulki.

Bugu da kari, lauyoyin kungiyoyin sun ce tarar tayi wa dokar kasashen Afrika da yarjeniyar kasashen Duniya a kan hakkokin siyasa hawan kawara.

Hukuncin NBC ya saba doka?

A karshe, an roki kotu ta umarci hukumar NBC ta kasa ta janye tarar Naira miliyan da aka ci talabijin domin a cewar masu shigar da kara, an saba doka.

Kara karanta wannan

Takarar Majalisa ta Dauki Zafi, Ana Sauraron Dawowar Tinubu Bayan Kwana 18 a Kasar Waje

Tashar ta ce ikirarin da Oluwadare, Nwankwo da Ogwuche suke yi shi ne ba za a haramtawa gidan talabijin yada labaran da za su taimaki jama'a ba.

Lauyoyin su na ganin Baba Ahmed yana da damar fadin abin da yake so, ya ce dokar NBC za ta rufewa mutane baki bayan tsarin mulki ya ba su ‘yanci.

Meya taimaki APC a zaben 2023

Farfesa Itse Sagay ya ce a kaf tarihin Najeriya, ba a taba yin wani zaben da ya fi na bana kyau ba, an rahoto shi yana cewa na’urorin BVAS sun yi aiki.

Itse Sagay yake cewa abin da ya taimaki Tinubu ya yi nasara shi ne, duk inda bai zo na farko ba, shi ne na biyu a baya, ya samu kuri’u da-dama a Arewa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel