LP: Yadda Aka Shiryawa Peter Obi Tarkon ‘Yan Mata da Kudi Domin Ganin Bayan Shi

LP: Yadda Aka Shiryawa Peter Obi Tarkon ‘Yan Mata da Kudi Domin Ganin Bayan Shi

  • Wani da ya yi aiki da Peter Obi a kwamitin yakin zaben 2023 ya ce babu irin tuggun da ba su gani ba
  • A cewarsa, sai da ta kai ana dasa mata a otel din da ‘dan takaransu zai sauka a lokacin yawon kamfe
  • Jam’iyyar LP ta hakikance cewa Obi bai yi amfani da addini domin samun goyon baya a takararsa ba

Abuja - Wani daga cikin ‘yan kwamitin yakin neman zaben jam’iyyar LP a takarar shugaban kasa, ya ce hukuma ta na neman ganin bayan Mr. Peter Obi.

Vanguard ta rahoto ‘dan siyasar yana cewa tun da aka fara yakin neman zabe, aka shiga kai wa ‘dan takararsu watau Peter Obi hari, domin a ga bayansa.

Wannan mutumi da ya yi magana da ‘yan jarida a boye, ya ce tun farko sun san da irin yunkurin da aka rika yi da nufin jam’iyyar LP ta gaza yin nasara.

Kara karanta wannan

An matsa mani lamba: Bayan tono asirinsa, Peter Obi ya fasa kwai game da zaben 2023

A cewarsa, an rika amfani da ‘yan mata iri-iri a matsayin tarko a otel din da ‘dan takaransu na shugaban kasa zai sauka, amma hakan bai iya tasiri ba.

An leka akawun a bankuna da salula

Baya ga mata da aka bullowa Obi da su, ‘dan kwamitin neman takaran yake cewa hukuma tayi ta laluben kudinsa a bankuna, a nan ma ba gano komai ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Da duk ba a ci nasara ba, sai yake cewa aka dauko badakalar Panama Papers, a karshe sai aka koma yi masa kutse ta salula, ana bibiyar kiran wayarsa.

Peter Obi
Peter Obi da Margaret Brownson Usen Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Jaridar ta rahoto Yunusa Tanko yana mai gaskata irin zargin, Kakakin kwamitin yakin zaben LP ya ce Obi yana fuskantar matsin lambar barin Najeriya.

Wata waya da ake zargin Obi da wani shahararren Fasto ta fito, amma Kakakin Jam’iyyar a yakin kamfen bana ya ce faifen da yake yawo na bogi ne.

Kara karanta wannan

Abin takaici: An kashe malamin addinin Muslunci daidai lokacin buda baki a wata jiha

Dr. Yunusa Tanko ya wanke ‘dan siyasar daga zargin da ake yi masa na amfani da addini a siyasa, yake cewa cancanta ce ta jawo aka zabi ‘dan takaransu.

Kakakin kwamitin yakin takarar ya ce ba kowa ba ne suka taso tsohon Gwamnan na jihar Anambra a gaba ba illa ‘ya ‘yan jam’iyyar APC dakuma jami’an tsaro.

Karar zaben shugaban kasa

A cewar Tanko, an koma amfani da jami’an tsaron kasar wajen yakar Obi, ana so a tursasa masa hakura da neman hakkinsa a kotun sauraron korafin zabe.

LP ta na kalubalantar hukumar INEC da APC a kan galabar da Bola Tinubu ya samu a zaben shugaban kasa, ta na zargin an saba doka kuma an shirya magudi.

Fanshon Gwamnonin Jihohi

Ku da labari cewa Gwamnoni irinsu Nyesom Wike, Ifeanyi Okowa, Udom Emmanuel, da Abdullahi Ganduje, za su bar ofis nan da ‘yan kwanaki kadan.

Kara karanta wannan

Tsohon Sarkin Kano, Sanusi Ya Fadi Munanan Barazanar da Ake Fuskanta a Yau a Najeriya

Haka kuma wa’adin Samuel Ortom, Darius Ishaku, da Nasir El-Rufai da wasunsu ya cika, za su rika karbar fansho, gidaje da motoci na sauka daga mulki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel