Ganduje, Matawalle, Wike Za Su Bar Mulki da Katafaran Gidaje da Dirka-Dirkan Motoci

Ganduje, Matawalle, Wike Za Su Bar Mulki da Katafaran Gidaje da Dirka-Dirkan Motoci

  • Gwamnonin 17 za su bar karagar mulki a ranar 29 ga watan Mayu 2023, wa’adinsu ya cika
  • Dokar jihohinsu tayi masu kayataccen tanadin fansho da motoci yayin da suke shirin ritaya
  • Wasu Gwamnonin sun yi wa’adi biyu da doka ta bada dama, akwai wanda ba zai zarce ba

Abuja - Punch ta fitar da rahoto a kan irin alheran da ke jiran wadannan Gwamnoni masu barin-gado yayin da mutanen jihohinsu ke cikin halin ha’ula’i.

Gwamnonin Ribas, Akwa Ibom, Kano, Jigawa, Zamfara, Kuros Riba, Abia, Ebonyi, Kaduna, Taraba, da Neja za su ci moriyar motoci, gidaje da fansho.

Haka abin yake ga Gwamnonin da za su bar ofis Jihohin Katsina, Sokoto, Kebbi, Filato da Enugu.

Bisa dokar jihar Ribas, Gwamna Nyesom Wike da mataimakiyarsa, Dr. Ipalibo Banigo za su samu motoci uku da za a rika canza masu duk bayan shekaru hudu.

Kara karanta wannan

Ayyuka 14 da Buhari Ya Yi wa Kudu da Babu Shugaban da Ya Kama Kafarsa a Tarihi

Fansho da alawus iri-iri

Za su rika karbar kudi daidai da albashinsu a matsayin fansho duk wata da 300% na albashin gwamnati a matsayin alawus na ayan daki, asibiti da shakatawa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sannan Wike da Banigo za su samu manyan gidaje biyu a duk inda suke sha’awa a fadin Najeriya.

Gwamnoni
Gwamnoni a Aso Rock Hoto: tribuneonlineng.com
Asali: UGC

A Zamfara, akwai N10m da tsohon Gwamna zai rika karba duk wata, mataimakinsa zai rika samun N5m. A lokacin Abdul-aziz Yari aka kara adadin kudin.

Aminu Tambuwal zai gaji abin da ‘yan bayansa su ke samu na N200m a duk shekara hudu. Baya ga haka za a rika biyan shi kudin kula da gida da barorinsa.

Babu marabar fansho da albashi

A Sokoto, tsohon Gwamna yana da motoci, kuma duk bayan shekaru hudu za a canza masa su. Fanshonsa da na mataimakinsa daidai ne da albashinsu a ofis.

Kara karanta wannan

Mulkin Tinubu: Jiga-jigan 'Yan Siyasa 3 Sun Hada Kai, Sun Fadi Wanda Suke So Ya Zama Shugaban Majalisa

Babu abin da zai canza a albashin Ikpeazu ko ya bar ofis a albashi, motoci zuwa dogaransa. Za a cigaba da kula da direba, barori, da masu dafa abincisa.

Dokar fanshon jihar Abia ta ba tsohon Gwamna da mataimkinsa damar zuwa asibiti idan su da bukata, gwamnati ce za ta dauki dawainiyar abin da aka batar.

Takarar Majalisa a 2023

Kusan mutum 10 su ke son zama Shugaban Majalisa a APC, rahoto ya zo cewa ‘yan adawa za su iya tsaida mutum daya, duk su mara masa baya ya yi nasara.

PDP, LP, APGA, YPP, NNPP da SDP sun yi taro saboda su yaki APC mai rinjaye. Muddin ‘ya ‘yan jam’iyyun hamayya suka dunkule, za su iya girgiza majalisar kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel