Tsohon Sarkin Kano, Sanusi Ya Fadi Munanan Barazanar da Ake Fuskanta a Yau a Najeriya

Tsohon Sarkin Kano, Sanusi Ya Fadi Munanan Barazanar da Ake Fuskanta a Yau a Najeriya

  • Tun bayan yakin Biyafara da aka yi a 1967-1970, ‘Yan Najeriya ba su taba rabuwa irin yanzu ba
  • Wannan shi ne ra’ayin tsohon Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II kamar yadda ya fada a taro
  • Da aka gayyace shi domin yin jawabi a bikin Ituah Ighodalo, Sanusi II ya ce ana cikin barazana

Abuja - Muhammad Sanusi II yana ganin cewa tun bayan yakin basasa, Najeriya ba ta taba samun kan ta a cikin rabuwar kai irin yadda ake a yau ba.

Punch ta rahoto tsohon Sarkin Kano yana cewa zabuka sun raba kawunan al’umma, an samu mummunan sabani ta fuskanar kabilanci da addini.

Tsakanin 1967 da 1970 aka yi yakin Biyafara a kasar nan, ‘yan bangaren Kudu maso gabas su ka nemi su balle daga Najeriya, amma hakan bai yiwu ba.

Kara karanta wannan

Innalillahi: 'Yan bindiga sun harbe shugaban APC a wata jiha, sun hallaka mazauna kauye

Muhammad Sanusi II yake cewa halin da aka shigan ya jefa alamun tambaya a kan ingancin wasu hukumomi da cibiyoyin gwamnati da ke Najeriya.

An yi wa INEC da Kotu tabo

A cewar Mai martaban, mutane su na dar-dar game da tsare-tsare da manufofin gwamnati, haka zalika ba a gamsu da ingancin hukumar zabe ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Rahoton ya ce Sanusi yana da ra’ayin al’umma ba su yarda da gaskiyar Alkalan kotun Najeriya ba.

Tsohon Sarkin Kano
Mai martaba Muhammad Sanusi II Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Ituah Ighodalo ya cika 62

Basaraken ya yi wannan bayani da yake jawabi a ranar Talata wajen wani taro da aka shirya domin taya Ituah Ighodalo murnar cika shekaru 62 a Duniya.

Ituah Ighodalo babban Fasto ne a cocin Trinity House da yake Legas. Tsohon Gwamnan na CBN ya halarci bikin da aka shirya ta kafar Zoom a jiya.

Kara karanta wannan

Mazan jiya: Hotunan gidan Tafawa Balewa sun jawo martani mai daukar hankali a intanet

Makasudin taron da aka yi shi ne a tattauna a kan yadda za a kawo gyara a harkar shugabanci, Sanusi II yana cikin masu gabatar da jawabi na musamman.

Baya ga rashin jituwa da aka samu tsakanin al’umma, har ila yau, tsohon Sarkin na Kano ya ce tattalin arzikin Najeriya ya shiga mawuyacin hali a yau.

Kamar yadda ya taba fada a wajen wani taro a Kaduna, Khalifa ya nanata cewa duk wanda zai mulki kasar nan bayan 2023, yana da jan aiki a gabansa.

Sanusi Lamido Sanusi a CBN

A wani rahoto da mu ka fitar, an ji cewa wadanda Bola Tinubu yake jin shawararsu, sun dage Sanusi Lamido Sanusi ya koma babban banki na CBN.

Babu mamaki zababben Shugaban ya nemi ya kori Godwin Emefiele idan an rantsar da shi musamman ganin yunkurinsa na canza kudi daf da zabe.

Kara karanta wannan

Ana Ramandan, Yan Addinin Gargajiya Sun Kai Hari Masallaci Sun Raunata Liman Da Wasu Mutane Da Dama A Osun

Asali: Legit.ng

Online view pixel