Kai Tsaye: Yadda Zaben Gwamna Ke Gudana a Jihohin Sokoto Da Neja
A yau Asabar, 18 ga watan Maris ne ake gudan da zaben gwamnoni da yan majalisar jihohi a fadin jihohi 28 cikin 36 na Najeriya.
Yan Najeriya za su sake komawa rumfunar zabe domin zabar wadanda suke so su jagorance su a matakin jiha na tsawon shekaru hudu masu zuwa.
A wannan zauren Legit.ng Hausa za ta kawo maku yadda zaben ke gudana a jihohin Sokoto da Neja.
Zaben gwamnan Neja
A jihar Neja za a fafata tsakanin yan takara 15 ne a zaben gwamnan na yau Asabar, sai dai ana ganin zaben zai fi zafi ne tsakanin jam'iyyar APC mai mulkin jihar, PDP, NNPP, LP da kuma APGA masu hamayya.
Muhammad Umar Bago shine dan takarar jam’iyyar APC a jihar Neja yayin da Isah Liman Kantigi ke rike da tutar PDP a jihar
Har ila yau a zaben gwamnan na Neja akwai kuma Yahaya Yahaya Sokodeke na NNPP. Jushua Bawa na LP da Khadija Iya Abdullahi a APGA da sauransu.
Zaben gwamnan Sokoto
Zaben gwamnan jihar Sokoto zai kasance daya daga cikin zabuka da za su dauki hankali sosai a fadin kasar kuma za a fafata ne tsakanin yan takara daban daban.
A yan takarar gwamnan jihar Sokoto, akwai Ahmad Aliyu Sokoto wanda ke rike da tutar jam'iyyar APC yayin da Sa'idu Umar ke rike da tutar PDP, Umar Dahiru Tambuwal na NNPP.
Sauran sune Ibrahim Muhammad Liman, dan takarar jam'iyyar ADP, Abubakar Umar Gada na jam'iyyar SDP da Aminu Umar Ahmad na Labour.
Janar Abdulsalami Abubakar ya kada kuri’arsa
Tsohon shugaban kasa a mulkin soja, Janar Abdulsalami Abubakar, ya kada kuri’arsa a garin Minna, babban birnin jihar Neja.
Dan takarar gwamnan PDP a Sokoto ya nuna karfin gwiwar shi zai yi nasara
Dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a jihar Sokoto, Mallam Saidu Umar, ya kada kuri’arsa a rumfar zabe ta 020 Ubandoma, Sabon-titi, Kofar Atiku ta Sokoto.
Da yake jawabi ga manema labarai jim kadan bayan ya kada kuri'arsa, Mallam Umar ya ce zuwa yanzu zaben na gudana cikin kwanciyar hankali da lumana yankunan jihar.
Ya ce zaben yau ya fi na shugaban kasa da aka yi yan makonni da suka gabata inda ya nuna karfin gwiwar cewa shine zai yi nasara a zaben, rahoton Thisday.
Dan takarar gwamnan APC a Neja ya kada kuri'arsa
Dan takarar gwamnan APC a jihar Neja, Muhammad Umar Bago ya isa mazabarsa inda ya kada kuri’arsa a zaben gwamna da na majalisar jiha da ke gudana.
Yadda guragu suka yi tururuwan fitowa zabe a Minna
Yayin da zaben gwamna ke ci gaba da gudana a jihar Neja, kungiyar masu lalurar nakasa sun ce ba za a barsu a baya ba.
An dai ga guragu da dama a wata rumfar zabe da ke garin Minna inda suka fito don sauke hakkinsu na yan kasa.
Tsohon gwamnan Neja ya kada kuri’arsa
Tsohon gwamnan jihar Neja, Muazu Babangida Aliyu, ya kada kuri’arsa a rumfar zabensa da ke unguwar Tunga a Minna, babban birnin jihar.
Rikici ya barke a wata rumfar zabe Karamar Hukumar Sokoto ta Arewa
An samu hatsaniya bayan wasu matasa sun hana jama’a yin zabe a wata rumfa da ke unguwar Dandima, Karamar Hukumar Sokoto ta Arewa.
Zabe a karamar hukumar Kontogora ta jihar Neja
Da misalin karfe 9:50, zabe na gudana a rumfar sakandare ta gwamnati a karamar hukumar Kontagora ta jihar Neja.
Hakazalika na’urar BVAS na tafiya daidaiba tare da kowani tangarda ba.
Yadda wakilin PDP a rumfar zabe ya kada kuri’a a madadin masu zabe a Sokoto
A rumfar zabe ta 008, Gidan Yumfa, jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke karamar hukumar Wamakko ta jihar Sokoto, an gano wakilin PDP a rumfar yana kada kuri’a a madadin masu zabe, kamar yadda Sahara Reporters ta rahoto.
An fara kada kuri’a a rumfar zabe ta Bakin-Iku a jihar Neja
A yanzu haka, jama’a sun fara kada kuri’a a rumfar zabe ta Bakin-Iku da ke Karamar Hukumar Tafa, a Jihar Neja kamar yadda jaridar Aminiya ta kawo.
Ana shirin fara zabe a rumfar zabe ta Lambar Tukera, karamar hukumar Sokoto
Da misalin karfe 8:33 na safe, jami’an INEC sun kammala duk wani tsare-tsare a gudunmar Tureka da ke karamar hukumar Sokoto.
Komai ya kammala tsaf a rumfar zabe ta Lambar Tukera inda ake shirin fara kada kuri’u.
An fara tantance masu zabe a karamar hukumar Sokoto ta kudu
Jama'a sun fara tururuwa zuwa rumfar zabensu a karamar hukumar Sokoto ta kudu.
Tuni jami'an hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) suka fara tantance masu kada kuri'a a yankin bayan masu zaben sun yi dogon layi.