Kamfanin MAGGI zai fara shiri na musamman a watan Ramadan
Ramadan wata ne da ke kara dankon kauna ga al'ummar Musulmi a fadin duniya. Lokaci ne da masoya cikin'yan uwa da abokai ke haduwa a lokutan sahur da buda baki, su ci abinci mai gina garkuwar jiki.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A irin wannan lokacin, ana bukar samun abinci mai inganci da dandano mai dadi – Abincin da zai kara dangon kauna yayin da 'yan uwa da abokan arziki suka hadu wajen cin abinci.
A cikin wannan shiri mai kayatarwa da MAGGI ya tanada a watan Ramadan, kwararrun mata biyar sun shirya tsaf domin shafe wata daya suna kawo shirye shiryen da za su sauya yadda kuke girki.
Matan za su gabatar da labaru guda shida a cikin wata daya domin koyar da yadda za a girka na'ukan abinci da za su dace da lokaci azumi.
Tare da fitattun jarumai da suka hada da Rekiya Attah da wasu, shirin Ramadan da MAGGI ya tanada ya zo da labaru masu cike da nishadi da darussa a tsawon makonni shida da za a fara a wannan watan.
Shirin zai haska kalubalen da mutane ke fuskanta a irin wannan lokacin, tare da bayyana yadda hadadden abinci ke tasiri wajen magance raunin zuciya, karfafa dangantaka a tsakanin al'umma. Yana da muhimmanci mu lura da cewa kusan kowa a cikin mu na fama da irin kalubalen, musamman a watan Ramadan da ake taruwa a ci abinci. Hakan na nuna cewa yana da kayau mu bibiyi shirin.
Kowanne bangare na shirin zai jaddada cewa haduwa da muke a Ramadan ba za ta gama cika ba sai an hada da son juna, alaka mai kyau, da fahimtar da tasirin da abinci ke yi a tsakaninmu. A cikin shirin, za mu fahimci yadda abinci ke tasiri wajen hada kan mutane su fahimci juna.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dangane da yadda MAGGI ke kokarin sada zumunci a tsakanin al'umma a watan Ramadan tsawon shekaru 10 da suka gabata, Manajan rukunin kamfanonin Nestlé a Najeriya, Rahamatou Palm-Zakari ta ce:

Kara karanta wannan
'Sun koma barayi': Ana zargin jami'an tsaron da gwamna ya kafa suna satar dabbobi
"Ramadan lokaci ne na kyauta, soyayya da raya dabi'u masu kyau da MAGGI ke shirye shirye domin karfafawa. Daga shirinmu da aka fi sani da MAGGI Diaries, mun kawo sabon shirin Tales of Ramadan, domin inganta alakar rayuwar masu amfani da kayayyakinmu. Ta hanyar samfuran kayan mu da girke-girkenmu, za mu ci gaba da tallafa wa mutane da iyalai wajen girka abinci mai kyau da inganci a ko da yaushe."
A matsayin kamfani mai samar da kayan abinci, MAGGI na da yakinin cewa dandano mai dadi yana yana da tasiri wajen gina jiki da sauya rayuwa.
MAGGI wani bangare ne na kamfanin Nestlé, kamfanin Good Food, Good Life, wanda ke da burin amfani da abinci don inganta rayuwar mutane a kowane lokaci.
Asali: Legit.ng