Mun Koyi Darasi a Zaben Shugaban Kasa, INEC Ta Bayyana Shirin Zaben Gwamnoni

Mun Koyi Darasi a Zaben Shugaban Kasa, INEC Ta Bayyana Shirin Zaben Gwamnoni

  • A yau ne INEC take shirya zabukan Gwamnonin jihohi da ‘yan majalisar dokokin jiha a Najeriya
  • Festus Okoye ya ce za a rika aika sakamakon zabe ta na’urar BVAS, sannan a hada da takarda
  • Kwamishinan yada labarai da wayar da kan masu zabe ya nuna Hukumar ta dauki darasi

Abuja - Hukumar INEC ta kasa ta yi bayanin yadda za a tattara sakamako daga mazabu a zaben Gwamnonin jihohi da ‘yan majalisar dokokin jiha.

Vanguard ta rahoto Kwamishinan yada labarai da wayar da kan masu zabe na INEC, Festus Okoye yana mai bayanin salon daukar sakamakon zabukan.

Festus Okoye ya yi wannan bayani ne da aka zanta da shi a tashar talabijin nan ta Arise a ranar Juma’a.

A wajen wannan tattaunawa ne Okoye yake cewa sun koyi muhimman darusa daga zabukan shugaban kasa da na ‘yan majalisar tarayya da aka yi.

Kara karanta wannan

'Dan takaran Sanatan APC a Kaduna Zai Tafi Kotu, Ya Fito da Hujjojin Magudin PDP

Abin da dokar ta ce a yau shi ne a aika sakamako ta hanyoyi dayan biyu, ko a tura ko a aika.

- Festus Okoye

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

BVAS.
Ana zabe da BVAS Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

Aikin PO da takardun EC8A

Kwamishinan na INEC yake cewa idan an kammala kada kuri’a a rumfuna, jami’in da ke kula da rumfar zaben zai shigar da sakamakon a takardar EC8A.

A wannan fam ne jami’in PO da INEC ta turo zai sa hannu kuma a buga hatimi, wakilan jam’iyyu za su sa hannunsu, kuma a ba ‘yan sanda takardarsu.
Daga nan kuma sai a dauki ainihin hoton EC8A da aka rattabawa hannu, a aika zuwa shafin duba sakamakon zabe na INECdomin al’umma su iya gani.
Ba hoton kurum za a tura ba, za a aika da takardun da kuma na’urar BVAS zuwa ofishin RAC.

- Festus Okoye

Kara karanta wannan

Zaben gwamnoni: Jihohi 28 ne za a yi zabe gobe Asabar, ga jerin sunayensu

Punch ta rahoto Okoye ya ce babban jami’in da yake tattara sakamako zai duba abin da yake cikin BVAS da takardun da aka kawo daga rumfunan yin zabe.

Kwamishinan ya ce a game da tura sakamako nan-take, sun koyi darasi daga zaben baya, kuma wannan karo za a rika tura sakamako da zarar sun fito.

Okoye ya sha alwashin cewa INEC za ta kara dagewa a zaben jihohin, ya kuma tabbatar da cewa an saita BVAS ta yadda ba za a samu wasu matsaloli ba.

Farfesa Hafiz Abubakar yana NNPP

Duk da ya raba jiha da Rabiu Musa Kwankwaso tun a shekarun baya, rahoto ya zo cewa Farfesa Hafiz Abubakar ya ce a zabi jam’iyyar NNPP a Kano.

Tsohon Mataimakin Gwamnan yana tare da Abba Kabir Yusuf da New Nigeria People’s Party a zaben yau, ya kuma zargi APC da shirin magudi.

Kara karanta wannan

Zaben gwamnoni: EFCC ta tirke Kano, Jigawa da Katsina da jami'anta, ta fadi dalili

Asali: Legit.ng

Online view pixel