Hajj 2024: Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Nada Sabon Amirul Hajjin Jihar Kano

Hajj 2024: Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Nada Sabon Amirul Hajjin Jihar Kano

  • Gwamnatin jihar Kano ta yi alkawarin ba kowanne maniyyacin jihar kyautar $500 a matsayin guzuri yayin da za su je sauke farali
  • Abba Kabir Yusuf ne ya sanar da hakan a lokacin da ya halarci taron bitar da aka yi wa mahajjatan a sansanin alhazai na jihar
  • Haka zalika, mai girma Abba Yusuf, ya nada mataimakin gwamnan jihar, Aminu Abdulsalam a matsayin Amirul Hajj na Kano a bana

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Yusuf ya nada sabon Amirul Hajj da zai jagoranci maniyyata aikin Hajjin Kano zuwa kasa mai tsarki domin sauke farali.

Abba Kabir Yusuf ya nada mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdulsalam Gwarzon a matsayin Amirul Hajj na jihar a bana.

Kara karanta wannan

Abin da muka sani game da hatsarin jirgin sama da ya kashe shugaban Iran

Gwamna Abba Yusuf ya nada Amirul Hajj na jihar Kano
Kano: Gwamna Abba Yusuf ya nada Amirul Hajj na bana. Hoto: @Kyusufabba
Asali: Twitter

Gwamnan wanda ya sanar da hakan a shafinsa na X ya kuma yi alkawarin gwangwaje maniyyatan jihar da kyautar dala 500 kowanne.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Za a ba mahajjan Kano kyautar $500

A jiya Litinin, mai girma Abba ya halarci bitar aikin Hajji da aka yi wa maniyyatan Kano, wanda aka yi a sansanin alhazai na jihar.

A cewar Gwamna Yusuf:

"Na yi amfani da wannan damar domin sanar da cewa kudin alawus na tafiye-tafiye ga maniyya zai zama $500 idan farashin Dala a kan Naira ya na a N1,250/$1.
"Mun yi wannan karamcin ne domin ba mahajjata damar gudanar da aikin Hajji ba tare da wata matsala ba."

An nada Amirul Hajj na Kano

Game da nadin Amirul Hajj na bana, gwamnan jihar na Kano ya ce:

"Na kuma sanar da cewa mataimakin gwamnan jihar, H.E Aminu Abdulsalam ne zai jagoranci tawagar gwamnatin jihar da alhazai zuwa aikin hajjin bana.

Kara karanta wannan

Harin masallacin Kano: Abba ya bayyana hukuncin da ya ke jira a yanke wa mai laifin

"Ina yiwa dukkanin mahajjata fatan alheri da kuma yin wannan tafiya cikin nasara."

Karanta sanarwar a kasa:

Gwamna Fintiri ya nada Amirul Hajj

A wani labarin makamancin wannan, mun ruwaito cewa gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri ya nada sabon Amirul Hajj na jihar.

A cikin wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar, mai girma Ahmadu Fintiri ya amince da nadin Mustapha Amin, Galadiman Adamawa a matsayin Amirul Hajji na jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel