Jam'iyyar ADC Ta Kori Dan Takararta Na Gwamna A Jigawa, Ta Mara Wa PDP Baya

Jam'iyyar ADC Ta Kori Dan Takararta Na Gwamna A Jigawa, Ta Mara Wa PDP Baya

  • Jam'iyyar African Democratic Congress, ADC ta kori dan takarta na gwamna a Jihar Jigawa bisa zargin zagon kasa tare da marawa jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, baya
  • Shugaban rikon kwarya na jam'iyyar ADC ne ya bayyana haka ga manema labarai a Dutse, tare da bayyana cewa PDP ce kadai zata iya ceto jihar daga rushewa
  • Dan takarar na ADC, Muhammad Gumel, ya ce shugaban rikon kwarya ba shi da ikon korarsa daga jam'iyyar, saboda tuni uwar jam'iyyar ADC ta kasa ta sallame shi

Jihar Jigawa - Jam'iyyar African Democratic Congress, ADC, a Jihar Jigawa ta kori dan takararta na gwamna a jihar, Muhammad Gumel, saboda zargin zangon kasa ga jam'iyyar, rahoton The Punch.

Mukaddashin shugaban jam'iyyar na jihar, Kabiru Hussaini, shi ne ya bayyana haka lokacin da ya ke zantawa da manema labarai a Dutse, babban birnin jihar, kamar yadda rahoton Daily Post ya bayyana.

Mustapha Sule Lamido
Jam'iyyar ADC Ta Kori Dan Takararta Na Gwamna A Jigawa, Ta Mara Wa PDP Baya. Hoto: The Guardian
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Hussaini ya roki yan jam'iyyar ta ADC da su zabi dan takarar PDP, Mustapha Sule Lamido, yana mai cewa jam'iyyar PDP ce kadai zata iya ceto jihar daga rushewa.

A cewarsa:

''Muna umartar duk magoya bayan jam'iyyarmu da su goyawa dan takarar gwamnan PDP baya saboda jam'iyyar PDP ce kadai zata iya ceto jihar daga rushewa gaba daya."

Dan takarar gwamnan na ADC, Gumel, an ruwaito cewa ya siyar da takararsa tare da goyawa jam'iyyar APC a jihar.

Da ya ke mayar da martani, Gumel ya ce shugaban rikon kwarya ba shi da ikon korarsa daga jam'iyyar.

Ya ce shugaban rikon kwarya tuni uwar jam'iyyar ADC ta kasa ta kore shi ranar 22 ga watan Satumba, 2022, kuma hukumar INEC da sauran hukumomin tsaro ba su san da zaman shi ba.

Kawancen da PDP ta yi da sauran jam'iyyu ba ya tada min da hankali, Uba Sani

A wani rahoton, Sanata Uba Sani ya ce hadin gwiwar da jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ta yi da wasu jam'iyyun siyasa a jihar ba ya tada masa da hankali.

Sani ya furta hakan ne yayin wata hira da shi da aka yi a gidan talabijin na Arise gabanin zabe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel