Zaben Gwamnoni: Jam'iyyar Accord Party Ta Koma Bayan APC a Jihar Legas

Zaben Gwamnoni: Jam'iyyar Accord Party Ta Koma Bayan APC a Jihar Legas

  • Neman tazarcen da gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), ya samu gagarumin tagomashi
  • Jam'iyyar Accord Party (AP) da dukkanin ƴan takarar ta sun janye sun koma bayan jam'iyyar APC a jihar
  • Jam'iyyar AP wacce a baya tayi ƙawance da Labour Party a jihar, tace ta dandara da irin cin kashin da jam'iyyar ta yiwa mambobin ta

Jihar Legas- Jam'iyyar Accord Party (AP) a jihar Legas ta nuna goyon bayan ta ga neman tazarcen da gwamna Babajide Sanwo-Olu, yake yi.

Jam'iyyar ta kuma sanar da hukuncin da ƴan takarar ta suka yanke na janyewa Sanwo-Olu da sauran dukkanin ƴan takarar APC a zaɓen ranar 18 ga watan Maris, 2023.

Sakataren watsa labarai na gwamnan Gboyega Akosile, a cikin wata sanarwa ya bayyana cewa shugaban jam'iyyar AP na Legas, Oladele Oladeji, yayi magana ne a wani taron manema labarai a Ikeja, ranar Talata. Rahoton The Cable

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Tashin Hankali Yayin da Jam’iyyun Siyasa 4 Ke Shirin Maja Don Tsige Gwamnan APC a Wata Jihar Arewa

Gwamnan Legas
Zaben Gwamnoni: Jam'iyyar Accord Party Ta Koma Bayan APC a Jihar Legas Hoto: Tribune
Asali: UGC

Oladeji ya bayyana cewa jam'iyyar ta ɓalle daga haɗakar ta da jam'iyyar Labour Party (LP) ne saboda yadda aka wulaƙanta mambobin ta bayan zaɓen shugaban ƙasa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya bayyana cewa ayyukan da Sanwo-Olu ya kwarara sune suka ja hankalin jam'iyyar wajen mara masa baya, wanda hakan ya nuna jam'iyyar bata da son rai amma tana bin cancanta ne. Rahoton Tribune

Yayi kira ga mambobin jam'iyyar AP da sauran mutanen jihar Legas da su fito kwansu da ƙwarƙwatar su a ranar Asabar, su zaɓi ƴan takarar jam'iyyar APC.

Da yake na shi jawabin, Peter Obayuwana, ɗan takarar gwamnan AP na jihar, yace ya haƙura da yin takara ne da gwamnan a dalilin ƙoƙarin da yayi wajen daƙile annobar cutar da sauran ayyukan cigaba da yayi a jihar.

Obayuwana yace jam'iyyar AP bata karɓa ba kuma bata nemi a bata ko asi ba kan wannan goyon bayan nata, inda ya ƙara da cewa wannan goyon bayan da zuciya ɗaya suka yi shi.

Kara karanta wannan

Ana Dab Da Zaɓen Gwamnoni, Jam'iyyu 5 Sun Koma Bayan Gwamnan APC Mai Neman Tazarce

Dubban ‘Ya’yan PDP Sun Sauya Sheka Zuwa SDP a Jihar Katsina

A wani labarin na daban kuma, dubunnan mambobin jam'iyyar PDP sun koma jam'iyyar SDP a jihar Katsina.

Wannan dai ba ƙaramin koma baya bane ga neman karɓe mulkin jihar da jam'oyyar PDP ke yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel