Idris Wase, Ben Kalu Da Wasu Mutum 3 Da Ke Neman Mukamin Kakakin Majalisar Wakilai

Idris Wase, Ben Kalu Da Wasu Mutum 3 Da Ke Neman Mukamin Kakakin Majalisar Wakilai

Gabannin rantsar da majalisar dokokin tarayya ta 10, yan majalisa biyar ne ke fafutukar neman mukamin kakakin majalisar wakilai, kamar yadda jaridar Vanguard ta rahoto.

Jaridar ta rahoto cewa shugabancin majalisar wakilan zai kasance a ajanda yayin da zababben shugaban kasa Bola Tinubu zai gana da zababbun mambobin majalisar wakilai a fadar shugaban kasa da ke Abuja a ranar Litinin, 13 ga watan Maris.

Yan majalisa da ke son zama kakakin majalisar wakilai ta 10
Idris Wase, Ben Kalu Da Wasu Mutum 3 Da Ke Neman Mukamin Kakakin Majalisar Wakilai Hoto: House of Representatives, Nigeria, Hon. Benjamin Kalu
Asali: Facebook

Wata majiya da Vanguard ta ambata ta ce za a duba tsarin karba-karba da addini wajen zabar kakakin majalisar na gaba, musamman kasancewar zababben Shugaban kasar da mataimakinsa duk musulmai ne.

Ga jerin sunayen masu neman takarar kujerar:

  1. Hon. Aliyu Betara (mazabar tarayya ta Biu/Kwaya, jihar Borno)
  2. Aminu Sani Jaji (mazabar tarayya ta Kaura Namoda/Birnin Magaji, jihar Zamfara)
  3. Hon. Idris Wase, mataimakin kakakin majalisar wakilai mai ci daga jihar Filato
  4. Ben Kalu, mai magana da yawun majalisar mai ci
  5. Ado Doguwa, shugaban masu rinjaye a majalisa ta tara.

Kara karanta wannan

Jerin Mukaman Da Gbajabiamila, El-rufai, Kudu Maso Gabas Ka Iya Samu a Gwamnatin Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matsayin Doguwa a majalisa ta 10

Legit.ng ta lura cewa Doguwa baya daga cikin zababbun yan majalisa ta 10.

Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta cire sunansa bayan baturen zaben ya ce ya ayyana Doguwa a matsayin wanda ya lashe zaben a cikin tashin hankali.

Dan majalisar wanda ya fito daga gidan gyara hali kwanan nan bayan an bayar da belinsa yana fuskantar zargi na kisan kai.

A halin da ake ciki, hukumar zaben ta ayyana cewa babu wanda ya lashe zabe a zaben majalisar dokokin tarayya na watan Fabrairu a mazabar Doguwa/Tudunwada.

Yadda Tinubu ke son kafa gwamnati mai damawa da kowa

A wani labarin kuma, mun ji cewa zababben shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya mayar da hankali sosai wajen ganin ya gina gwamnati da za ta dama da kowani yanki na kasar gabannin rantsar da shi.

Kara karanta wannan

Da walakin: Tinubu zai gana da zababbun 'yan majalisu da sanatoci kan wata bukata daya

Majiyoyi masu karfi sun ce Tinubu zai muka kujerar shugaban majalisar dattawa zuwa kudu maso gabas don dinke barakar da ke tsakani na ganin cewa ana mayar da su saniyar ware a kasar.

Ana kuma ganin zai bai wa tsakanin Gwamna Nasir El-rufai da Gwamna Abdullahi Ganduje mukamin babban sakatern gwamnatin tarayya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel