Hasashen Zaben Gwamna: PDP Zata Lashe Jihohi 15, APC Zata Lashe 10

Hasashen Zaben Gwamna: PDP Zata Lashe Jihohi 15, APC Zata Lashe 10

Kungiya fafutuka ta Enough is Enough (EiE) da SB Morgen (SBM) Intelligence sun saki sakamakon binciken da suka gudanar game da wadanda zasu lashe zaben gwamnonin da za'ayi.

A ranar 11 ga Maris, yan Najeriya zasu zabi wadanda zasu jagoranci jihohinsu da kuma mambobin majalisun jiha.

Za'a gudanar da zabn gwamnan ne a jihohi 28.

A rahoton cewa kungiyoyin sun yiwa lakabin: 'Hasashen EiE-SBM Intelligence: Zaben gwamnoni', sun bayyana jam'iyyun da zasu lashe kowace jiha.

Zaben Najeriya
Zaben Najeriya Hoto: INEC
Asali: UGC

Rahoton yace mutum 8,921 aka tattauna dasu game da zaben shugaban kasa, gwamnoni da yan majalisu tsakanin ranar 16 ga Junairu da 3 ga Febrairu, 2023.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewar wani rahoto na EiE:

Kara karanta wannan

Jerin Duka Shugabannin PDP 9 da Aka Yi Rabuwar Tsiya da Su Daga 1999 zuwa 2023

"Tsakanin 16 ga Junairu da 3 ga Febrairu, 2023, SBM Intelligence ta tattauna da mutum 8921 game da zabukan shugaban kasa, gwamnoni da yan majalisu."
"Hakazalika mun tattauna da mutum 2,613 ta wayar tarho. An tattauna da su ne a dukkan jihohin Najeriya 36 da Abuja. Game da zaben gwamnoni, mun zabi tattaunawa da mutane ido da ido."

Ga sakamakon binciken:

Jihohin da PDP zata ci

1. Sokoto

2. Kebbi

3. Oyo

4. Katsina

5. Kaduna

6. Bauchi

7. Gombe

8. Adamawa

9. Cross River

10. Akwa Ibom

11. Rivers

12. Delta

13. Taraba

14. Ebonyi

15. Plateau

Jihohin da PDP zata ci

1. Borno

2. Yobe

3. Jigawa

4. Zamfara

5. Niger

6. Kwara

7. Nasarawa

8. Benue

9. Ogun

10. Lagos

Jihohin da LP zata ci

1. Abia

Jihohin da NNPP zata ci

1. Kano

Jihohin da PDP zata ci

1. Enugu

Kara karanta wannan

Jam’iyyar APC ta Kunshe Biliyoyin Kudi Wajen Saida Fam Ga Masu Sha’awar Takara

Jerin jihohin PDP, APC, LP da NNPP suka ci a zaben shugaban kasa

A zaben shugaban kasar da aka yi a karshen makon da ya gabata, an samun sabbin jam'iyyu biyu da suka taka rawar gani.

Wadannan jam'iyyu sun hada da Labour Party da kuma New Nigeria Peoples Party NNPP.

Jam'iyyar Labour Party LP ta samu nasarar lashe zabe a jihohi 12 yayinda NNPP ta samu nasarar lashe jiha daya kacal.

Jam'iyyar All Progressives Congress APC hakazalika ta lashe zabe a jihohi 12, kamar dai yadda jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP ta lashe jihohi 12.

Asali: Legit.ng

Online view pixel