"Kwankwaso Gwarzo Ne" NNPP Ta Maida Martani Kan Nasarar Tinubu

"Kwankwaso Gwarzo Ne" NNPP Ta Maida Martani Kan Nasarar Tinubu

  • Jigon jam'iyyar NNPP mai kayan marmari, Buba Galadima, ya ce Kwankwaso ne gwarzon zaben shugaban kasa da aka kammala
  • Galadima ya yi ikirarin cewa taron dangi aka yi wa Kwankwaso ta kowane ɓangare kama daga INEC da jam'iyyun siyasa
  • INEC ta ayyana cewa NNPP ta samu kuri'u miliyan 1.4m baki ɗaya amma jigon yace a Kano kaɗai ya haura haka

Jigon jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), Buba Galadima, ya ce ɗan takararsu na shugaban kasa, Rabiu Musa Kwankwaso ne gwarzon zaben da aka gudanar ranar Asabar.

Galadima ya caccaki hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) bisa rashin sanya suna da tambarin NNPP a jikin takardar kuri'a, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Rabiu Musa Kwankwaso
Dan takarar shugaban kasa a inuwar NNPP, Rabiu Kwankwaso Hoto: RMK
Asali: Facebook

Jigon NNPP kuma tsohon abokin shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya yi wannan furucin ne yayin hira da Arise TV ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: INEC Ta Bayyana Wanda Ya Samu Nasara a Karamar Hukumar Gwamna Wike

A kalamansa, Buba Galadima ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Kwankwaso gwarzon jarumi ne, shi kaɗai ya tsaya, INEC ta yaƙe shi a rumfunan zabe."
"Kunsan kuwa babu NNPP da takardun kuri'a? Kun san babu tambarin jam'iyya? Mutane basu gane alamar kayan marmari a cikin kwando. Kwandon da aka sa kamar jirgin ruwa."

Galadima ya kara da cewa baki ɗaya manyan jam'iyyu uku sun sa NNPP a gaba sun yi kokarin ganin bayanta.

Bugu da ƙari, jigon siyasan ya yi ikirarin cewa Kwankwaso ya samu kuri'u Miliyan ɗaya da rabi a Kano kadai, amma INEC ta ayyana cewa jimullan kuri'un da ya samu miliyan 1.4m.

"Kafin ranar zabe, manyan jam'iyyu uku sun yi duk yadda zasu yi su ga bayan jam'iyyar NNPP. INEC ta ce kuri'u miliyan 1.4m Kwankwaso ya samu, amma zan iya bugun kirji na faɗa maku kuri'a 1.5m ya samu a Kano kadai."

Kara karanta wannan

Zaben 2023: "Duk Wanda Bai Gamsu Da Sakamako Ba Ya Tafi Kotu", Martanin INEC Ga PDP Da LP

Wasu Abubuwa Da Suka Taimaka Wajen Rashin Nasarar Kwankwaso

A wani bangaren kuma mun tattara maku muhimman abubuwan da suka ja Kwankwaso ya sha ƙasa a zaben shugaban ƙasa 2023

Rabiu Musa Kwankwaso, tsohon gwamnan Kano ya samu kuri'u kusan miliyan ɗaya da rabi a zaben da ya gudana ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023.

Ɗan takarar na jam'iyyar NNPP ya zo na huɗu a jerin masu yawan kuri'u. Mun tattara maku wasu batutuwa da ake ganin sun taimaka wajen kai shi ƙasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel