Zaben 2023: "Duk Wanda Bai Gamsu Da Sakamako Ba Ya Tafi Kotu", Martanin INEC Ga PDP Da LP

Zaben 2023: "Duk Wanda Bai Gamsu Da Sakamako Ba Ya Tafi Kotu", Martanin INEC Ga PDP Da LP

  • Hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta fada wa jam'iyyun siyasa da suka nuna ba su gamsu da zabe ba su tafi kotu
  • Farfesa Mahmood Yakubu, shugaban hukumar INEC ne ya furta hakan, biyo bayan korafi da jam'iyyun PDP, NNPP da wasu suka yi game da zaben
  • Mahmood ya ce ba daidai bane wani mutum ko jam'iyya ta yi kokarin datse wa hukumar aikin ta da doka ta bada damar yi don haka su bi tsari su tafi kotu

FCT Abuja - Hukumar zabe mai zaman kanta na Najeriya, INEC, ta ce jam'iyyun da suka korafi kan sakamakon zabe su tafi kotu, rahoton The Cable.

A ranar Litinin Dino Melaye, wakilin PDP, da na wasu jam'iyyan sun fita daga wurin tattara sakamakon zabe na kasa a Abuja kan jinkirin INEC na dora sakamakon zabe kan kundin bayanai na yanar gizo na (IRev).

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Yi Wa Yan Najeriya Babban Alkawari A Jawabinsa Bayan Lashe Zabe

Mahmood Yakubu.
Mahmood Yakubu, shugaban INEC yana rike da makirfon yana jawabi. Hoto: The Cable
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Melaye, ya kuma zargi Mahmood Yakubu, shugaban INEC, da yin rashin adalci.

Ita ma jam'iyyar Labour ta kira taron manema labarai a Transcorp Hilton Hotel, ta yi kira ga Yakubu ya yi murabus a matsayin shugaban INEC.

Jam'iyyun kuma sun bukaci a sake sabon zaben shugaban kasa, suna cewa wanda aka yi 'babu adalci da nagarta.'

Martanin Hukumar INEC

Da ya ke mayar da martani, cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Rotimi Oyekanmi, babban sakataren shugaban INEC, ya ce kiran da aka yi wa Yakubu ya yi murabus 'rashin sanin ya kamata ne.'

INEC ta kuma ce ikirarin da Melaye ya yi na cewa ciyaman din INEC ya ba wa wata jam'iyya kuri'u ba gaskiya bane kuma rashin sanin ya kamata ne.

Kara karanta wannan

2023: Jam'iyyar NNPP Ta Kwankwaso Ta Fada Wa INEC Ta Soke Zabe, A Sake Sabo

Sanarwar ta ce:

"Akasin abin da wasu jam'iyyun siyasa ke zargi, sakamako da suka fito daga jihohi sun nuna cewa an yi zaben adalci kuma mai nagarta.
"Akwai tsari da aka samar ga jam'iyyu or yan takara wadanda ba su gamsu ba game da sakamakon zabe. Ba za a amince da furta maganganu da za su iya tada zaune tsaye ba.
"An kusa kammala aikin zaben. Idan adalci za a yi zai jam'iyyun da ba su gamsu ba su bari a kammala aikin sannan su tafi kotu da hujojinsu su nemi hakkinsu."

Asali: Legit.ng

Online view pixel