Duniya Rawar Ƴan Mata: Lalong Ya Tunkuyi Ƙasa a Takarar da Yayi Ta Sanata

Duniya Rawar Ƴan Mata: Lalong Ya Tunkuyi Ƙasa a Takarar da Yayi Ta Sanata

  • Gwamnan da Yaso Ya Shige Ofishin Sanata daga Kujerarsa ta Gwamna Kai Tsaye ya Haɗu da Cikas.
  • Gwamnan na Plato, Yasha Ƙasa ne a Hannun Ɗan Takarar Jam'iyyar PDP Mai Suna Napoleon Bali a Cikin Wani Yanayi na Bazata
  • Da Alama Dai Gwamnan Bai Tsammani Hakan Ba, Duba da Yana da Karfin Faɗa A Jihar Ta Plateau.

Jos - Ita duniya kamar yadda ɗan Hausa yake faɗi, rawar yan mata ce. Duniya juyi juyi ce wai kwaɗo ya jishi a cikin ruwan zafi.

Hakan nada alaƙa akan yadda ake ta samun saukale a siyasar ƙasar nan, biyo bayan kammala zaɓen Shugaban Ƙasa dana ƴan majalisa da aka ƙaddamar a asabar din data gabata.

Babban Darakta janar na yaƙin neman zaɓen Tinubu/Shettima kuma gwamnan Jihar Plateau Simon Lalong shima yasha ƙasa a ƙoƙarin sa na zuwa majalisar dattawan Najeriya.

Kara karanta wannan

A Kwantar Da Hankali, Kada a Kaiwa Igbo Hari, Inji Tinubu akan Rashin Nasararsa a Legos

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Lalong
Simon Lalong Ya Tunkuyi Ƙasa a Takarar da Yayi Ta Sanata Hoto: Legit.ng
Asali: UGC

Lalong yasha kayi ne a hannun ɗan takarar jam'iyyar PDP mai suna Napoleon Bali.

Jaridar Vanguard ta ambato cewa Lalong yayi takara a cikin inuwar jam'iyyar APC kuma ya samu ƙuria guda 91, 674, yayin da Bali wanda yayi nasara ya samu ƙuri'u 148,844.

Idan dai za'a iya tunawa, tun a tashin farko me dai, Lalong ya rasa akwatin sa dake Ajikamai ga jam'iyyar Labor Party da kuma Shendam ta tazara mai matuƙar yawa.

Budu da ƙari, Isaac Kwallu ya samu gagarumar nasara a Mikang/Shendam/Qua’an Pan wanda ya bashi damar nasara akan Lalong da kuma John Dafa’an, yaro a wajen Lalong kafin su raba gari wanda yayiwa jam'iyyar APC.

Yan Daban Siyasa Sun Kona Mutum Biyu Da Ransu a Ofishin NNPP a Kano

Abubuwan mamaki na cigaba da faruwa a Jihar Kano, yayin da wasu yan daba suka kone mutane biyu da ransu ƙurmus.

Kara karanta wannan

INEC Ku Daure, Ku Cije Akan Gaskiya Karku Bari Matsin Lamba Yayi Tasiri Akan Ku - Atiku Abubakar

Haka zalika ofishin NNPP dake yankin da abin ya faru yasha wuta, inda ya ƙone ƙurmus.

Shima ofishin INEC anyi ƙoƙarin ƙone shi, amma abin yaci tura bai afku ba saboda jami'an tsaron da aka jibge a wajen tattara sakamakon.

Asali: Legit.ng

Online view pixel