INEC Ku Daure, Ku Cije Akan Gaskiya Karku Bari Matsin Lamba Yayi Tasiri Akan Ku - Atiku Abubakar

INEC Ku Daure, Ku Cije Akan Gaskiya Karku Bari Matsin Lamba Yayi Tasiri Akan Ku - Atiku Abubakar

  • Tsohon Mtataimakin Shugaban Kasar Ya Zargi Jam'iyyar APC Mail Mulki Da Matsawa INEC lamba akan Sakamakon Zabe
  • Atiku Abubakar yayi ikirarin yiwa Jam'iyyar APC mai mulki Fintinkau a Arewa - Maso Yamma da kuma Arewa Maso Gabas
  • Shugaban Kuma Tabbatar Da Cewa Zasu Dangana Ga Nasara Idan Har Aka Bar INEC Tayi Aikin ta Batare Da Matsin Lamba ba

Abuja - Ana ta amsar sakamakon zaɓen shugaban ƙasa dana ƴan majalisun da akayi ranar Asabar ɗin data gabata. Jam'iyyu da yan takarkari nata maida martani akan yadda lamarin zaɓen ya wakana.

Wasu ƴan takarkarun kuma INEC ɗin suke takala akan yadda ta gudanar da zaɓen nata haɗi da hanyar data biyo wajen tattare sakamakon zaɓe.

Hakan masana na ganin ka iya tasiri ga hukumar INEC wajen gudanar da ayyukan da take tsaka dashi na tattara sakamakon zaɓen da akayi.

Kara karanta wannan

A Kwantar Da Hankali, Kada a Kaiwa Igbo Hari, Inji Tinubu akan Rashin Nasararsa a Legos

Atiku
INEC Ku Daure, Ku Cije Akan Gaskiya Karku Bari Matsin Lamba Yayi Tasiri Akan Ku - Atiku Abubakar Hoto: Vanguardngr
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

To saidai a wani salon irin na dattaku da nuna ƙwarewa ta siyasa, tsohon shugaban ƙasa Alhaji Atiku Abubakar kuma ɗan takarar jam'iyyar PDP ya fito yayiwa INEC tausar ƙirji.

Daraktan tsare-tsare da sadarwa na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓe na Atiku da Okowa, Dele Momodu, ne yayi wannan batu a garin Abuja.

Inda yayi kira da INEC da kada ta saduda akan yadda Jam'iyyar APC mai mulki take mata bawan ƙawara tare da matsin lamba akan ta canja ra'ayin yan Najeriya da suka bayyana batare da takurawa ba'a ranar Asabar ɗin data gabata.

To amma duk da haka, Kwamatin yaƙin neman zaɓen na Atiku, ya yabawa INEC abisa jajircewa tun daga lokacin da aka soma fuskantar zaɓe zuwa yau.

Saƙon na Atiku Abubakar ta bakin Momodu ya nuna cewa, anyiwa Jam'iyyar APC mai mulki mahangurɓa a Arewa - Maso Yamma da kuma Arewa Maso Gabas.

Kara karanta wannan

Mun gano INEC Na Ƙirƙirar Ƙuri'un Shafcin Gizo-da-Koƙi - Shugaban Labor Party

Bugu da ƙari, yace har a yankin Kudu maso Gabas anyi wa jam'iyyar ta APC illa a siyasance.

Sakon ya tabbatar da cewa, da wannan alƙaluma da suke dashi, suna da tabbacin cewa, babu yadda za'a yi APC ta samu nasarar maida adadin kuri'un da suka rasa a wannan yankin mai yawan jama'a.

Jaridar Vanguard ta tabbatar da cewa, Momodu ya bada misali da yadda PDP take yin gagarumin nasara yankuna da dama na najeriya, amma banda Kudu maso Gabas inda Jam'iyyar Labor Party take cin karen ta babu babbaka.

A cewar sa, Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP ne kawai zai iya cika ƙa'idar samun ƙuri'u da ake so a samu ta kaso 25 a ciki ɗari na aƙalla jihohi 25 a cikin yankunan siyasa daban-daban na ƙasar da ake dasu.

Saboda haka, yana kan matsayar ganin nasara tasu ce kamar yadda bayanin Momodu ya zayyana.

Kara karanta wannan

Yanzu: Jam'iyyar Labor Party Tayi Kira Da Soke Zaɓen Shugaban Ƙasa

Shin ko kunsan Gwamnonin Enugu Da Cross River Sun Fadi Zaben Sanata?

Gwamnonin Enugu Da Cross River Sun Fadi Zaben Sanata

Gwamnan PDP, Ifeanyi Ugwuanyi ya sha kaye a zaben Sanatan da aka gudanar asabar din data gabata inda ɗan takarar Labour Party, Okechukwu Ezea ya ci zaben a jihar Enugu.

Hakazalika, Gwamna Ben Ayade na jihar Cross River bai yi nasara ba'a kokarinsa na son komawa majalisar dattawan Najeriya.

Ayade wanda ya kasance dan APC ne ya sha kaye a hannun sanata mai ci, Jarigbe Agom-Jarigbe ne duk a zaben da aka gudanar a ranar asabar din data gabata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel