Tsohon Shugaban Amurka Ya Aikowa 'Yan Najeriya da Sako Za a Shiga Filin Zabe

Tsohon Shugaban Amurka Ya Aikowa 'Yan Najeriya da Sako Za a Shiga Filin Zabe

  • Muhimmancin zaben 2023 ya jawo Barack Obama ya aiko da jawabi na musamman ga Najeriya
  • Tsohon Shugaban Amurkan ya bukaci shugabanni da ‘yan takara su tabbatar an yi zabe mai inganci
  • Obama ya ce dama ta samu da mutane za su zabi wadanda suke so ba tare da an jawo tashin-tashina ba

America - Tsohon Shugaban kasar Amurka, Barack Obama ya yi kira da babban murya ga al’umma, ‘yan takara da shugabannin Najeriya a kan zabe.

A ranar Talata, Daily Trust ta rahoto Barack Obama cewa ya bukaci ayi zabe na gaskiya da adalci, ba tare da an kawo tashin-tashina da rigingimu ba.

Obama yake cewa Najeriya ta shiga cikin mawuyacin hali, amma tayi nasara a kan kalubalen domin a yau, tattalin arzikinta ya fi na kowace kasa a Afrika.

Kara karanta wannan

Gaskiya ta fito: Sarki Sanusi ya tona asirin abin da aka kitsa wajen sauya fasalin Naira

Tsohon shugaban na Amurka ya ce a zaben sabon shugaban kasa da sauran zabukan da za ayi, al’umma sun samu damar bude wani sabon babi a Najeriya.

Jawabin Barack Obama

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Barkanku dai, a yau ina so in yi magana kai tsaye da ku, mutanen Najeriya. Najeriya babbar kasa ce da za ku yi alfaharin irin cigaban da ku ka samu.
Kun samu ‘yancin kai, kun baro mulkin soja, kun karfafa tsarin mulkin farar hula. Kun yi kokarin magance sabaninku, ku maida shi silar karfinku.
Tsohon Shugaban Amurka
Shugaban Najeriya yana gaisawa da Barack Obama Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Kun yi kokari sosai wajen inganta rayuwar jama’a, kun kafa tattalin arziki mafi girma a Afrika.
Yanzu dama ta samu a tarihi da za ku yi rubutu a sabon babin cigaban Najeriya ta hanyar kada kuri’a a zabukan nan da za a gudanar.
Idan ana so zabe ya zama mai inganci, ya zama dole ayi adalci da gaskiya da zaman lafiya. Dole a ba duk ‘Dan Najeriya damar yin zabe.

Kara karanta wannan

Daga karshe: Saura kiris zabe, Limaman Katolika sun fadi wadanda za su zaba a zaben bana

Saboda haka ina kira ga shugabanninta da masu neman takara su raba magoya bayansu da rigima domin kuwa ba ta wuri a harkar zabe.

- Barack Obama

An rahoto Obama yana kira ga jama’a su gujewa masu tada rikici, su tabbatar an zauna lafiya ba tare da la’akari da wanda ya yi nasara wajen lashe zaben ba.

A jawabinsa, Obama ya ce ta hanyar zabe ne za a magance matsalolin da suka addabi kasar.

IGP ya yi Sauye-sauye a Kano da Ribas

A jihar Ribas, an ji labari Kwamishinoni hudu za su tare domin ganin an yi zabe cikin zaman lafiya. IGP ya dauke Kwamishinan jihar, ya maida shi zuwa Enugu.

Kakakin ‘yan sanda na Kano, Abdullahi Kiyawa ya ce Muhammad Yakubu, Ita Uku-Udom da Abaniwonda Olufemi su ne Kwamishinonin da aka turowa jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel