Kwankwaso Zai Dura Kano Domin Yin Yawon Kamfen Karshe a Yakin Zaben 2023

Kwankwaso Zai Dura Kano Domin Yin Yawon Kamfen Karshe a Yakin Zaben 2023

  • Rabiu Musa Kwankwaso zai iso Kano domin ya kammala yawon yakin neman zaben shugaban kasa
  • ‘Dan takaran Shugaban kasar na Jam’iyyar NNPP ya gama zagaye Jihohi, zai rufe kamfe a Mahaifarsa
  • Magoya baya za su tarbo tsohon Gwamnan a Kwanar Dangoro a ranar da APC za tayi gangamin karshe

Kano - Rabiu Musa Kwankwaso mai neman zama Shugaban Najeriya a karkashin jam’iyyar NNPP zai shigo mahaifarsa ta Kano a ranar Alhamis.

A wani gajeren jawabi da ya yi a shafinsa na Twitter a yammacin Laraba, Rabiu Musa Kwankwaso ya tabbatar da cewa yana shirin rufe yakin kamfe.

‘Dan takaran yake cewa bayan ya dauki wata da watanni yana zagaye lungunan kasar nan, zai iso garin Kano domin ya yi taron kamfen na karshe.

Rabiu Musa Kwankwaso ya gayyaci daukacin al’umma zuwa wajen wannan babban gangami.

Kara karanta wannan

Manya Alkawura 3 Da Nike Yiwa Yan Najeriya Idan Na Zama Shugaban Kasa, Kwankwaso

"Ina gayyatar kowa" - RMK

“Bayan shafe watanni mu na karada kasar nan, mu na tattaunawa da ‘Yan Najeriya daga kowane lungu da sako.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A gobe (Alhamis) zan isa Kano domin gangamin yakin neman zabenmu na karshe. Ina gayyatar kowa ya zo.

– RMK

Kwankwaso
Taron NNPP a Hadejiya Hoto: @KwankwasoRM
Asali: Twitter

Majiyarmu ta shaida mana tun kusan karfe 11:30 na daren yau, Rabiu Kwankwaso da tawagarsa suka isa garin Kaduna domin shirin karasowa Kano.

Kafin ya baro birnin tarayya Abuja a jiya, ‘dan takaran ya ziyarci garin Dutse inda ya yi wa sabon Sarki murna da kuma ta’aziyyar rashin mahaifinsa.

'Yan NNPP da APC za su hade a Kwanar Dangoro?

Da karfe 10:00 na safen yau ne magoya bayan darikar Kwankwasiyya da ‘ya ‘yan jam’iyyar NNPP za su hadu a Kwanar Dangoro domin gangamin.

Sai dai kuma ‘yan jam’iyyar APC mai mulki a jihar Kano sun tsaida yau dinnan a matsayin ranar karshe da suke yawon yakin neman zaben 2023.

Kara karanta wannan

Gaskiya ta fito: Sarki Sanusi ya tona asirin abin da aka kitsa wajen sauya fasalin Naira

Wani hadimin Gwamnan Kano, Abubakar Aminu Ibrahim ya tabbatar da haka a shafinsa.

'Mun rufe kamfe' - Abba Gida Gida

A gefe guda, Darektan harkokin yada labarai a kafofin zamani na kwamitin yakin neman zaben Gwamnan Kano a NNPP, ya ce sun gama yawon kamfe.

Salisu Yahaya Hotoro ya sanar da cewa sun rufe zagayen yawon ƙananan hukumomi 44, abin da ya rage shi ne su tarbo Kwankwaso Kwanar Ɗangora a yau.

Akwai yiwuwar ayi kicibis?

Ibrahim Adam Hadimi ne ga Rabiu Kwankwaso, ya shaida mana ba wani taro za a shirya ba, magoya baya ne kurum za su raka mai gidansa zuwa gida.

A zantawarmu da shi, Adam ya ce ba su da labarin APC za tayi gangami sai a jiya, ya kuma ce sun sanar da jami’an tsaro tun kwanaki uku da suka wuce.

Hadimin ya ce ba za a fasa yi wa ‘dan takaran na NNPP maraba ba, ya ce ya ragewa jami’an tsaro su tabbatar da zaman lafiya da kuma kwanciyar hankali.

Kara karanta wannan

2023: Jerin Sunayen Manyan Malaman Addini Da Ke Takara a Zabe Mai Zuwa

Asali: Legit.ng

Online view pixel