Ibrahim Khaleel, Idahosa, Alia, Da Sauran Malaman Addini Da Ke Takara a Zaben 2023

Ibrahim Khaleel, Idahosa, Alia, Da Sauran Malaman Addini Da Ke Takara a Zaben 2023

Yayin da babban zaben shugaban kasa ke kara gabatowa, yan takara da jam’iyyunsu na siyasa sun dukufa wajen yakin neman zabensu a fadin kasar.

Sai dai kuma, wasu shugabannin addinin Musulunci da Kirista sun ajiye akidarsu don shiga siyasa da takara a zaben 2023, inda suke neman kuri’uns mutanensu.

Malaman addini
Ibrahim Khaleel, Idahosa, Alia, Da Sauran Malaman Addini Da Ke Takara a Zaben 2023 Hoto: Bishop Isaac Idahosa
Asali: Twitter

Ga jerin wasu daga cikin shugabannin addini da ke takara a zaben:

Bishop Isaac Idahosa

Malamin addinin shine abokin takarar Rabiu Musa Kwankwaso, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar New Nigerian Peoples Party (NNPP) a zabe mai zuwa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A wata hira da shi, Idahosa ya bayyana cewa ya fara tunanin tsayawa takarar kujerar siyasa kafin aka bayyana shi a matsayin abokin takarar Kwankwaso.

Sheikh Malam Ibrahim Khaleel

Kara karanta wannan

Majalisar Malaman Kasar Yarbawa Sun Shirya Addu'a Ta Musamman Don Nasarar Tinubu

Malamin musuluncin mazaunin Kano wanda ke neman takara a zabe mai zuwa ya dade ana damawa da shi a siyasar jihar.

Shine shugaban kungiyar malaman Kano. A kwanaki ne ya sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa ADC inda ya zama dan takarar gwamnan jam’iyyar.

Rev. Fr. Hyacinth Lormem Alia

Ya kasance daya daga cikin manyan malaman da suka bar yin wa’azi suka koma siyasa, shine dan takarar gwamnan APC a jihar Benue a zabe mai zuwa.

Alia ya shafe shekaru 32 a darikar Katolika kafin ya shiga siyasa a 2022. Ya yi suna saboda shirinsa na wakar da mutane wanda yake yi a Saint Thomas Parish Catholic Church da ke Anum a Makurdi.

Usani Usani

Tsohon ministan harkokin Neja Delta ya kasance shahararren fasto a jihar Cross Rivers kuma dan takarar Gwamnan jam’iyyar PRP a zabe mai zuwa.

Ya shafe tsawon lokaci a matsayin Fasto a cocin Liberty da ke Calabar har zuwa lokacin da ya shiga siyasa lokacin da ya fara zama kwamishina a jihar.

Kara karanta wannan

Saura kwana 5: Kungiyar Arewa ta AFC ta fadi dan takarar da take so ya gaji Buhari

Sauran malaman da ke takarar siyasa a Calabar sune:

  1. Essien Ayi, yana takarar zarcewa a kujerarsa ta dan majalisar wakilai mai wakiltan mazabar Akpabuyo/Bakassi/Calabar.
  2. Ogar Osim, dan takarar gwamnan jihar karkashin Labour Party, ya rike babban mukami a cocin Patriarch Christ Shepherd.

Pastor Umo Eno

Shine kwamishinan fili da albarkatuin ruwa kuma dan takarar gwamnan jihar Akwa Ibbom karkashin Peoples Democratic Party (PDP).

Gwamna mai ci kuma shugaban kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na PDP, Udom Emmanuel ne ya tsayar da shi.

A wani labarin, jam'iyyar PDP reshen jihar Kano ta rasa manyan jiga-jiganta inda suka sauya sheka zuwa jam'iyyar NNPP ana gab da zabe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel