"Zan Soke Tsarin Sauya Fasalin Naira Idan Na Hau Mulki", Kwankwaso

"Zan Soke Tsarin Sauya Fasalin Naira Idan Na Hau Mulki", Kwankwaso

  • Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yiwa yan Najeriya alkawarru guda 3 masu muhimmanci
  • Saura kwanaki biyu yan siyasa su kammala kamfe kamar yadda dokar zabe na INEC ta bukata
  • Kwankwaso na cikin manyan yan takara hudu a zaben shugaban kasa da zai gudana ranar Asabar

Funtua - Dan takaran shugaban kasa karkashin jam'iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP), Senator Rabiu Musa-Kwankwaso, ya yiwa yan Najeriya alkawarin share musu hawaye idan ya hau mulki.

Kwankwaso ya ce zai soke tsarin sauya fasalin Naira, zai magance matsalolin tsaro kuma ya dakile yunwa.

Kwankwaso zai fafata da sauran yan takara ranar Asabar, 25 ga Febrairu, 2023.

KWankwaso
Zan Soke Tsarin Sauya Fasalin Naira Idan Na Hau Mulki, Kwankwaso Hoto: Rabiu Kwankwaso
Asali: Depositphotos

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Tsohon gwamnan jihar Kanon ya bayyana hakan ne yayin jawabi ga dubunnan masoya jam'iyyar NNPP a garin Funtua, jihar Katsina, rahoton ThisDay.

Kara karanta wannan

Yan Kwanaki Kafin Zabe: PDP Ta Hadu Da Gagarumin Cikas a Kano, Tsagin Shehu Sagagi Sun Yi Maja Da Jam’iyyar Kwankwaso

Ya bayyana cewa zai amince yan Najeriya su mayar da dukka tsaffin kudinsu banki idan yayi nasara.

Ya yi bayanin cewa wannan tsari na bankin CBN zai sakejefa yan Najeriya cikin mangin talauci duk da cewa yanzu haka akwai mutum milyan 33 da ke fama da bakin talauci.

Yace:

"An fada mana cewa akwai yan Najeriya milyan 133 amma suka kawo sauyin fasalin Naira a wannan lokaci mai muhimmanci na zabe. Wannan tsari ya jefa talakawa da dama cikin kunci, yunwa, wahala.
"Amma idan kuka zabeni matsayin shugaban kasar nan tare da sauran yan takaran NNPP, mun yi alkawarin kawo karshen wannan doka kuma zamu bari ku kai tsaffin kudadenku bankuna don ajiya ko harkokinku."
"Mu a NNPP na shirin yiwa yan Najeriya mulkin kwarai, samar da zaman lafiya, magance tsaro, da inganta tattalin arziki."

Ya ce jam'iyyar NNPP na da ikon kawo karshen rashin tsaro a fadin kasa.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Yan Bindiga Sun Jefa Bam Ofishin Yan Sanda, Sun Hallaka Jami'ai 3

Hakazalika zasu dauki dimbin matasa matsayin jami'an tsaro domin kawo karshen matsalar.

Babu ruwanmu da APC, PDP a takarar 2023 - 74% na masu bibiyar shafin Legit.ng

Legit.ng Hausa ta gudana da zaben jin ra'ayi na musamman domin sanin inda makaranta shafinta suka sa a gaba.

An wallafa kuri'ar ga masu bibiyar shafinmu a Twitter kuma su zabi wanda suke ganin zai yi nasara a zaben ranar Asabar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel