2023: Dan Majalisar Tarayya Ya Jingine Dan Takarar Jam'iyyarsa, Ya Koma Bayan Tinubu

2023: Dan Majalisar Tarayya Ya Jingine Dan Takarar Jam'iyyarsa, Ya Koma Bayan Tinubu

  • Ɗan majalisar wakilan tarayya a inuwar jam'iyyar ADC ya ayyana goyon baya ga ɗan takarar shugaban ƙasa na APC, Bola Tinubu
  • Ɗan majalisar wanda ya hito daga jihar Kogi, ya kira Tinubu da mutum mai kayutata wa kuma ba zai iya juya masa baya ba
  • A cewarsa, Tinubu ya fi dukkanin yan takara cancanta kuma yana da yakinin zai ɗaga martabar Najeriya

Abuja - Yayin da ake tunkarar 2023, mamban majalisar wakilan tarayya kuma jigon jam'iyyar ADC, Hon. Leke Abedije, ranar Jumu'a ya ayyana goyon bayansa ga Bola Tinubu na jam'iyyar APC.

Abejide, shugaban kwamitin kula da kwastam na majalisa, ya bayyana haka ne yayin da ya kai ziyarar bazata wurin taron masu ruwa da tsakin APC daga Kogi ta yamma wanda ya gudana a Abuja.

Kara karanta wannan

2023: "Ka Ci Zaɓe Ka Ci Zabe" Yadda Dubun Dubatar Magoya Baya Suka Yi Maraba da Tinubu a Jihar Arewa

Honorabul Abejide.
2023: Dan Majalisar Tarayya Ya Jingine Dan Takarar Jam'iyyarsa, Ya Koma Bayan Tinubu Hoto: @HouseNGR
Asali: Twitter

Taron wanda wakilin Legit.ng Hausa ya halarta, ya gano cewa Abejide, mamba mai wakiltar mazaɓar Yagba, ya halarci wurin tare da Chief Dare Maiyegun da wasu kusoshin ADC a Kogi.

Ɗan majalisar tarayyan ya kuma jaddada aniyarsa ta aiki tukuru don masarar Bola Tinubu duk da ya san martabarsa a matsayin mamban majalisa a inuwar ADC.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A kalamansa yace:

"Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ne ɗan takarana kuma mai taimaka mun, ina da kowane dalili da ake nema kan marawa Tinubu baya. Ku duba nasarorin da ya samu a jihar Legas, wanda ya nuna cancantarsa da mulkar Najeriya."
"Ban damu da duk abinda za'a ce ba ko da hakan zai sa na rasa kujerata ni da mutanen mazaɓata zamu goyi baya kuma mu zaɓi Asiwaju a 2023 mai zuwa."

Haka zalika a wurin ya ba da tallafin Naira miliyan N3.5M ga matasan APC waɗanda suka halarci taron, yace su raba a tsakanin kananan hukumomi 7 da suka haɗa Kogi ta yamma.

Kara karanta wannan

Yan Najeriya Sun Samu Sabon Sumfurin Shugaba Buhari, Doguwa Ya Jaddada Wanda Ya Dace da Mulki a 2023

Matsala a Gidan Kwankwaso, Ɗan Takarar Mataimakin Gwamna Ya Yi Murabus

A wani labarin kuma ɗan takarar mataimakin gwamna a inuwar NNPP a jihar Neja ya janye daga takara a 2023 Bayan janye wa daga takara, Bahago, ya kuma sanar da ficewar daga jam'iyya mai kayan marmari, ya miƙa godiya bisa nuna masa kauna.

Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan ɗan takarar shugaban kasa a NNPP, Rabiu Kwankwaso, ya yi ikirarin cewa shi ke da nasara a zabe mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262