Babu Ruwanmu Da Kwankwaso, Tinubu Zamu yi: Cewar Yan Takaran Jam'iyyar NNPP a Jihar Osun

Babu Ruwanmu Da Kwankwaso, Tinubu Zamu yi: Cewar Yan Takaran Jam'iyyar NNPP a Jihar Osun

  • Da alamun jam'iyyar NNPP da dan takararta sun shiga matsala gabanin zaben shugaban kasa a 2023
  • Jigogin jam'iyya a wata jihar kudu sun bayyana cewa su fa Tinubu za su yi, ba Kwankwaso ba
  • Sanata Rabiu Kwankwaso na cikin mutum hudu da ake ganin zasu iya nasara a zaben Febrairun 2023

Osogbo - Yan takarar kujerun majalisar dokokin tarayya da jiha karkashin jam'iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, a jihar Osun sun yi watsi da dan takarar shugaban kasansu, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Sun bayyana goyon bayansu ga Asiwaju Bola Tinubu na All Progressives Congress, APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

Hakazalika sun shirya taron gangami na musamman a Osogbo, babban birnin jihar don nuna goyon bayansu ga Tinubu.

Vanguard ta ruwaito cewa Afolabi Muideen, ya bayyana hakan a jawabin da ya fitar a madadin yan majalisan.

Kara karanta wannan

'Dan Majalisar Tarayya Ya Jingine 'Dan Takarar Jam'iyyarsa, Yace Tinubu Zai Wa Aiki a 2023

Ya ce sun gano al'ummar jihar Osun fa basu yarda da Kwankwaso da jam'iyyar NNPP ba tukun.

Kwankwaso
Babu Ruwanmu Da Kwankwaso, Tinubu Zamu yi: Cewar Yan Takaran Jam'iyyar NNPP a Jihar Osun
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Afolabi, wanda ke takarar kujerar majalisar jiha mai wakiltar Ifelodun, ya ce sun yanke shawaran goyon bayan Tinubu ne saboda wannan dalili.

A cewarsa:

"Yayin kamfen gida-gida da muke gudanarwa, mun gano cewa al'ummar jihar Osun fa Asiwaju Bola Tinubu suke so ya zama shugaban kasa kuma yiwa wani dan takara daban kamfe tamkar batawa kai lokaci ne, shi yasa muka ce mu ma Tinubu zamu yi."
"Yan takarar kujerun majalisar dokokin tarayyarmu tuni sun yi watsi da Kwankwaso, yan takaran kujerun majalisar jiha 9 zasu shirya taron gangami don Tinubu."
"Muna jinjinawa Sakataren kwamitin yakin neman zaben Tinubu/Shettima, Hanarabul James Faleke, wanda ya karbe mu hannu biyu-biyu bayan gano irin gudunmuwar da zamu baiwa Tinubu ya kashe Osun."

Kara karanta wannan

Gwamnonin G5: Wasu gwamnonin PDP Na Shirin Komawa APC? Gaskiya Ta Bayyana

Yan takaran sun hada da: Afolabi Muideen Abayomi (Ifelodun), Opeyemi Amoo (Ife North), Babalola Timothy (Ila), Adelowokan Festus (Ilesha west), Ibrahim Adebisi (Ilesha east), Owoduni Emmanuel (Atakumosa east /west), Adekehinde Modupe Omolola (Oriade) da Odeyemi Tumininu ( Obokun)

Shugaban Kasa a 2023: APC da PDP Sun Mutu Murus, Ni Za Ku Zaba, Kwankwaso Ga Yan Najeriya

A wani labarin, dan takarar shugaban kasa Rabiu Kwankwaso ya bukaci masu zabe da su yi waje da APC sannan kada su zabi PDP a zabe mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida

Online view pixel