Sabon Ciwon Kai Ga Atiku: Jigon PDP Shema Ba Zai Yiwa Atiku Kamfen Ba a Katsina

Sabon Ciwon Kai Ga Atiku: Jigon PDP Shema Ba Zai Yiwa Atiku Kamfen Ba a Katsina

  • Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, zai gabatar da yakin neman zabensa a jihar Katsina a yau Talata
  • Ana rade-radin jagoran PDP a Katsina, Ibrahim Shema da mabiyansa za su kauracewa kamfen din babbar jam'iyyar adawar kasar
  • Ba'a ga maciji tsakanin tsohon gwamnan da dan takarar gwamna na jam'iyyar a zaben 2023, Sanata Yakubu Lado Danmarke

Katsina - Tsohon gwamnan jihar Katsina kuma shugaban PDP a jihar, Barista Ibrahim Shehu Shema tare da mambobin kwamitin uwar jam'iyyar a jihar 10 cikin 14 da ciyamomin kananan hukumomin jihar 19 cikin 34 na iya kauracewa gangamin kamfen din Atiku Abubakar.

A yau Talata, 20 ga watan Disamba ne za a gudanar da yakin neman zaben shugaban kasa na babbar jam'iyyar adawar a jihar Katsina.

Atiku Abubakar
Sabon Ciwon Kai Ga Atiku: Jigon PDP Shema Ba Zai Yiwa Atiku Kamfen Ba a Katsina Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Martanin kwamitin yakin neman zaben Atiku-Lado

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Tashin hankali ga Tinibu, Atiku ya samu wata ganawa da Kiristocin wata jihar Arewa

Vanguard ta rahoto cewa hakan ya saba ma ikirarin da shugaban kwamitin yakin neman zaben Atiku-Lado, Sanata Umar Ibrahim Tsauri, ya yi yayin da yake jawabi ga manema labarai a ranar Lahadi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsauri ya ce:

"Zan so ku yarda sannan ku aminta da ni cewa PDP kanta a hade yake kuma a shirye take ta kai Najeriya zuwa inda take mafarkin kaiwa."

Hakazalika, a taron manema labaran, Darakta Janar na kwamitin kamfen din Atiku-Lado, Dr Mustapha Muhammad Inuwa ya ce:

"Tsakaninsa da tsohon gwamna, sun yarda su ajiye banbancin ra'ayinsu da kuma aiki tare don fatattakar APC daga karagar mulki a zaben 2023."
"Bari na tabbatar maku da cewar a ranar Alhamis da ya gabata, Ina ganin mun shafe sama da awa 2 muna tattaunawa da tsohon Gwamna, Ibrahim Shema kuma mun yarda kan abu guda, shine fatattakar APC daga mulki.

Kara karanta wannan

2023: An Yi Zaman Sulhu da Gwamna Wike Na Karshe, Sakamakon Ya Ja Atiku Ya Ɗauki Babban Mataki

"Mu dukka biyu mun yarda kuma mun tabbata abun da mutanen jihar ke so shine mu hada hannu don cimma hakan.
"Kafin wannan haduwar, ina so ku sani cewa sama da shekaru 15 kenan bamu hadu ko yin magana da juna ido da ido ba. Amma mun hadu yanzu, mun zauna, mun tattauna sannan mun fayyace lamura da dama.
"Don haka ku kwantar da hankalinku cewa zai shiga cikin dukka harkokin da muka fada maku. Babu wani abun ta da hankali yanzu, watakila har sai bayan ziyarar Atiku sannan idan ba a gan shi ba, sai mu fara fadin dalilin da yasa wane da wane basu hallara ba."

Har yanzu abubuwa basu daidaita ba a PDP reshen Katsina, Lawal Uli

Da yake martani ga jawabin a hira da Vanguard, mukaddashin shugaban PDP a Katsina, Salisu Lawal Uli, ya saka ikirarin shugabannin na kwamitin yakin neman zaben Atiku-Lado a shakku yayin da ya ce har yanzu abubuwa basu daidaita ba a PDP reshen Katsina.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC Ta Samu Gagarumin Tagomashi, Dubban Mutane Sun Sauya Sheka A Jihar Sokoto

Uli ya ce:

"Idan ikirarinsu gaskiya ne, tun jiya da yau suke shirye-shirye, ba a sanar da mafi yawan jiga-jigan jam'iyyar, shugabannin kwamitin jihar da mambobin 10 cikin 14 komai ba game da batun ziyarar da dan takarar shugaban kasar zai kawo? Kuma me yasa ciyamomin kananan hukumomi 19 cikin 34 basu shiga tsarin ba?

Da aka tambaye shi idan yan bangaren Shema za su halarci gangamin kamfen din Atiku, Uli ya ce:

"Idan baka da masaniya a kan taron ta yaya za ka shiga ciki, ta yaya za ka hallara a wurin?"

Alaka ta yi tsami tsakanin tsagin Shema da tsagin dan takarar gwamnan jam'iyyar, Sanata Yakubu Lado Danmarke saboda banbancin ra'ayi, lamaein da yasa Uli da wasu mambobin kwamitin aiki na PDP a jihar su takwas zuwa kotu don neman hakkinsu.

Buhari ya mun alkawarin tabbatar da sahihin zabe

A wani labarin, Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na PDP ya nuna karfin gwiwar lashe zabe a 2023 domin a cewarsa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi masa alkawarin tabbatar da sahihin zabe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel