2023: Jam'iyyar APC ta karbi karin masu sauya sheka a Sokoto

2023: Jam'iyyar APC ta karbi karin masu sauya sheka a Sokoto

  • Gwamna Aminu Waziri Tambuwal shine shugaban gwamnonin Nigeria, kuma shine shugaban yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP a jihar Sokoto.
  • Siyasar Sokoto dai ta dau dumi duba da yadda tsohon gwaman jihar da kuma gwamna mai ci ke fafatawa da tsahon gwamna jihar Wamakko.
  • Sauyin sheka gabanin zabe ba bakon al'amari bane a tsakanin 'yan siyasa a Nigeria.

Sokoto: Jam'iyyar APC, mai adawa a jihar Sokoto, tace ta karbi karin wasu masu sauya sheka daga jam'iyyar PDP da sauran jam'iyyu zuwa jam'iyyarta a arewacin shiyyar jihar.

Wannan na kunshe cikin wata takarda da mai taimakawa tsohon gwamna jihar ya rabawa manema labarai yau Jumu'a a Sokoto.

A cewar sanarwar dubban masu sauyin shekar sun fito ne daga yankuna Gwadadawa, da Wamakko da sauran kananan hukumomin da suke shiyyar Sokoto ta arewa.

Kara karanta wannan

Kwabar Atiku ta yi ruwa, ya rasa manyan shugabannin PDP a wata jihar Arewa

“Wanda suka sauya shekar sun hada da tsoffin kansiloli, da masu rike da mukamai a jam;iyyar da suka baro".
“Gaba daya wanda suka sauya shekar sun sami tarba tun daga matakin karamar hukumarsu da kuma tarba ta musamman daga dan takarar gwamna jihar da mataimakinsa,” .

Sanarwar ta kara da cewa sauyin shekar zai baiwa jam'iyyar kwarin gwuiwa da fatan samun nasara a zaben shekarar 2023, kamar Yadda jaridar The Nation ta rawaito.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sokoto
2023: Jam'iyyar APC ta karbi karin masu sauya sheka a Sokoto
Asali: UGC

Aiyukan Buhari Ne Sukasa Jam’iyyar Farin Jini

Da yake jawabi a wajen taron, Maigari Dingyadi, ministan harkokin ‘Yan sanda, ya bayyana ci gaban a matsayin nasara, bayan nasarorin da gwamnatin tarayya karkashin jam’iyyar APC ta samu.

“Gwamnatin APC karkashin kulawa shugaba Muhammadu Buhari ta kawo ayyukan ga kasa masu inganci da nufin yin tasiri ga rayuwar jama’a."

Kara karanta wannan

Ta karewa Tinubu a Arewa, Atiku ya karbi mambobin APC 10,000 zuwa APC a jihar Arewa

Jaridar Vanguard tace Dingyadi bai gushe ba sai da yace:

“Gwamnati ta shafe shekaru bakwai da rabi tana ayyuka da shirye-shirye masu tasiri ga rayuwar marasa galihu a kasar nan".

Asali: Legit.ng

Online view pixel