Baya ta Haihu: Gwamnatin Abba ta Musanta Labarin Harbin dan Jarida a Kano

Baya ta Haihu: Gwamnatin Abba ta Musanta Labarin Harbin dan Jarida a Kano

  • Gwamnatin jihar Kano ta musanta cewa harsashin bindiga ne ya jikkata wani dan jarida Naziru Idris Ya'u a gidan gwamnati da yammacin Juma'a
  • Rahotanni da fari sun yi zargin an harbi wani dan jarida a fadar gwamnatin Kano jim kadan bayan sun dawo daga aiki su na hutawa a bakin masallaci
  • Amma a martanin da Sunusi Bature Dawakin Tofa, darakta janar kan yada labaran Gwamna Abba Kabir Yusuf ya fitar, ya ce karfe ne ya soki hannun dan jaridar

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kano- Gwamnatin jihar Kano ta musanta zargin harsashi ya samu wani dan jarida a gidan gwamnati a karshen makon nan.

Kara karanta wannan

Borno: Gwamna Zulum ya tafka babban rashi yayin da hadiminsa ya rasu

Naziru Idris Ya’u, wani dan jarida da kafar talabijin din Abubakar Rimi (ARTV) na zaune da sauran 'yan jarida ne kawai ya ce ya ji wani abu ya soke shi, wanda aka bayyana da cewar alburushi ne.

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf
Gwamnatin Kano ta musanta an harbi dan jarida a fadar gwamnati Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

A sakon da ya wallafa a shafinsa na facebook, darakta janar ka yada labaran Gwamna Abba Kabir Yusuf, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya ce babu batun harbi a fadar gwamnatin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kano: "Karfe ne ya soki 'dan jarida," Sunusi

A karin hasken da fadar gwamnatin Kano ta sanarwar da Sunusi Bature Dawakin Tofa, darakta janar kan yada labaran Gwamna Abba Kabir Yusuf ya fitar, ya ce wani karfe ne ya soki Naziru.

Sunusi Bature Dawakin Tofa ya kara da cewa wani aiki ake yi a kusa da gidan gwamnatin.

A cewar Sunusi Bature Dawakin Tofa, ana tsaka da aikin ne wani karfe ya yi tsalle ya soki dan jaridar a hannu, kamar yadda Leadership News ta wallafa.

Kara karanta wannan

An harbi wani dan jarida a gidan gwamnatin Kano, bayanai sun fito

Saboda haka ne ma Darakta janar din ya bayyana labarin harsashi ya soki dan jaridar da ba dai-dai ba.

Sai dai ya ce tuni aka kai Naziru Idris Ya'u asibitin da ke fadar gwamnatin jihar, kuma an duba lafiyarsa.

An harbi dan jarida a hannu a Kano?

A baya mun kawo muku cewa Naziru Idris Ya'u ya gamu da iftila'i bayan wani abu da ake kyautata zaton harsashi ne ya same shi a hannu.

Rahotanni sun bayyana cewa Naziru da sauran 'yan jarida na wurin da ake alwala dab da masallacin dake fadar gwamnatin ne sai aka ga abu ya soke shi a hannu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel