Rikicin PDP: Atiku Ya Ɗauki Babban Mataki Bayan Zaman Sulhu na Karshe da Wike, G5

Rikicin PDP: Atiku Ya Ɗauki Babban Mataki Bayan Zaman Sulhu na Karshe da Wike, G5

  • Abubuwa sun sake rikirkicewa tsakanin Atiku Abubakar da tawagar Wike watau G5, waɗanda suke takun saka da shugabancin PDP
  • Bayanai sun nuna cewa Atiku ya yanke shawarin cigaba da harkokinsa ba tare goyon bayan G5 ba gabanin zaɓen 2023
  • Majiya tace Atiku ya maye gurbin gwamna Makinde na Oyo da Gwamna Adeleke a matsayin kodinetan kudu maso yamma

Rivers - Wasu majiyoyi masu alaka da zaman sulhu tsakanin Atiku Abubakar da tawagar gaskiya watau G5 sun bayyana cewa ɗan takarar shugaban kasa a inuwar PDP ya cigaɓa da shirin tunkarar zaɓen 2023.

Ɗaya daga cikin majiyoyin da ta samu zantawa da jaridar The Nation ranar Lahadi, 18 ga watan Disamba, 2022 tace tuni Atiku ya fara ɗaukar matakai a kwanitin kamfen PDP.

Gwamna Makinde, Atiku da Adeleke.
Rikicin PDP: Atiku Ya Ɗauki Babban Mataki Bayan Zaman Sulhu na Karshe da Wike, G5 Hoto: thenationonline
Asali: UGC

Tace Atiku ya maye gurbin gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo da gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun a matsayin Kodinetan kamfe na shiyyar kudu maso yamma.

Kara karanta wannan

Gwamnonin G5: Wasu gwamnonin PDP Na Shirin Komawa APC? Gaskiya Ta Bayyana

A cewar majiyar, tsohon mataimakin shugaban kasan ya yanke haka ne bayan zaman sulhun da aka yi tsakaninsa da gwamnonin G5 a Patakwal, babban birnin jihar Ribas.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ce zaman wanda ake ganin shi ne na karshe ya gudana ne a gidan gwamna Wike dake Patakwal kuma Atiku ya samu wakilcin Gwamnan Adamawa, Ahmadu Fintiri.

Dole Ayu ya yi murabus - G5 na nan kan bakarsu

A wurin taron, gwamna Wike ya jaddada cewa sauke Ayu daga shugabancin PDP ne kaɗai sharaɗin da zai sa su goyi bayan burin Atiku na zama shugaban ƙasa a 2023.

Gwamnonin G5 sun kafe kan matsayarsu duk da rokon da gwamna Fintiri ya masu su yi hakuri a matsa gaba kuma a maida hankali wurin taimakawa Atiku ya lashe zaɓe.

Majiyar tace:

"Kowane ɓangare tsakanin wakilan Atiku da na G5 sun san cewa wannan ne zaman sulhu na karshe da nufin lalubo bakin zaren da ɗinke ɓarakar cikin gida."

Kara karanta wannan

Tinubu ko Peter Obi? An Fadi Dan Takarar da Gwamna Wike Zai Mara Wa Baya Bayan Raba Gari da Atiku

"Abu ɗaya da Fintiri ya iya tabbatarwa a madadin Atiku shi ne gwamnonin guda 5 su yi hakuri su jira har sai ɗan takarar shugaban ƙasa ya samu nasara sannan Ayu ya yi murabus."
"Amma kamar yadda aka saba, G5 sun yi watsi da wannan tayin kana suka kafe cewa ya zama tilas Ayu ya yi gaba."

Daga yanayin yadda abubuwa ke tafiya, kowane ɓangare sun amince da zahiri, Atiku ya ci gaba da shirye-shiryen tunkarar 2023 ba tare da goyon bayan G5 ba.

APC ta kara karfi a Jigawa

A wani labarin kuma Jam'iyyar PDP Ta Rasa Daruruwan Mambobinta a Gundumar Tsohon Gwamnan Jigawa

Bayanai sun nuna cewa aƙalla mambobin PDP 200 ne suka sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki a yankin karamar hukumar Birnin Kudu.

Sun samu tarba mai kyau daga mataimakin shugaban karamar hukumar Birnin Kudu, Alhaji Yusuf Isa Wurno.

Asali: Legit.ng

Online view pixel