Ondo: Yadda Matar Malamin Addini da Wasu Mutum 2 Suka Kuɓuta Daga Hannun Ƴan Bindiga

Ondo: Yadda Matar Malamin Addini da Wasu Mutum 2 Suka Kuɓuta Daga Hannun Ƴan Bindiga

  • Ƴan sanda sun damƙe ƴan bindiga biyar bayan sun yi garkuwa da matar malamin coci da wasu mutum biyu a jihar Ondo
  • Rahoto ya nuna barci ne ya kwashe masu garkuwar har mutanen da suka sace suka samu nasarar arcewa ba tare da sun sani ba
  • Kwamishinan ƴan sandan jihar Ondo ya ce nan ba da jimawa ba za a gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Ondo - Dakarun ƴan sanda sun samu nasarar cafke mutum biyar da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a jihar Ondo.

Waɗanda ake zargin sun shiga hannu ne yayin da barci ya sace su bayan sun yi garkuwa da matar wani malamin coci da wasu mutum biyu.

Kara karanta wannan

An rasa rayuka bayan bam ya tashi da 'yan kai amarya a jihar Borno

Yan sandan Najeriya.
Mutum uku sun kubuta bayan bacci ya kwashe ƴan bindigar da suka sace su a Ondo Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa masu garkuwan sun kama barci ne bayan sun sha wasu miyagun ƙwayoyi, lamarin da ya bai wa matar faston da sauran mutum biyu damar tsere wa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Miyagun masu garkuwar da ƴan sandan suka kama sun haɗa da Garuba Mumuni, 27; Yusuf Tale, Kabiru Muhammed, Shaibu Umar da kuma Adamu Mohammed.

Yadda ƴan sanda suka kama 'yan bindiga

Rundunar ƴan sandan jihar Ondo ta bayyana cewa jami'an caji ofis na Ofosu ne suka kama ƴan bindigar bayan samun bayanai kan inda suka ɓuya.

A cewar rundunar tun farko jami'an ƴan sanda sun samu rahoton cewa an yi garkuwa da wata matar Fasto da mutum ɗaya a coci yayin da aka sace mutum na uku yana tsaka da aiki a gona.

Rundunar ƴan sandan ta ce:

"Amma waɗanda aka yi garkuwa da su sun samu nasarar arcewa daga hannun miyagun a ranaku daban-daban bayan masu garkuwar sun sha kwayoyi sun kama barci.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi awon gaba da malaman addini suna kan hanyar zuwa yin wa'azi

"Bayan tattara bayanan sirri, dakarun ƴan sandan Ofosu suka damƙe waɗanda ake zargi mutum biyar kuma mutanen da aka sace ɗin sun tabbatar da cewa sune suka yi garkuwa da su."

Ƴan sanda za su gurfanar da 'yan bindiga

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Abayomi Oladipo, ya ce nan ba da jimawa ba za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu, rahoton Daily Post.

Jirgin sojoji ya samu nasarori

A wani rahoton na daban Rundunar sojin saman Najeriya (NAF) ta ce ta samu nasarar kakkabe 'yan ta'adda da dama a hare-haren da ta kai Borno da Neja.

Kakakin rundunar NAF, AVM Edward Gabkwet ya bayyana cewa jiragen yaki sun kashe 'yan ta'adda da lalata makamansu a Chinene.

Asali: Legit.ng

Online view pixel